Home Back

Ina Takaicin Yadda Ƴan Jarida Ke Shan Wahala – Shugaban Kamfanin Jaridar LEADERSHIP Zainab Nda-Isaiah

leadership.ng 5 days ago
Ina Takaicin Yadda Ƴan Jarida Ke Shan Wahala – Shugaban Kamfanin Jaridar LEADERSHIP Zainab Nda-Isaiah

Shugabar Ƙungiyar kafofin ƴada Labarai ta LEADERSHIP, Zainab Nda-Isaiah, ta bayyana damuwarta kan yadda ƴan jarida da marubuta  ke fama da ƙamfar kuɗi da sukuni, duk kuwa da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen fito da ra’ayin jama’a da kawo sauyi a cikin al’umma.

Da take jawabi a wajen taron baje kolin littafin “Rubutu don Kafafan Yada Labarai da Samun Kuɗi” na Azubuike Ishiekwene, ta jaddada rashin jin daɗin halin da marubuta da yawa suke fuskanta na talauci duk da ayyukan da suke yi masu muhimmanci.

Ta yi imanin cewa littafin Ishiekwene zai ba da haske mai mahimmanci da kuma koyar aiki don taimakawa marubuta su guje wa cusa kai cikin duhu da wahalar samun kuɗi.

Zainab ta bayyana littafin a matsayin cikakken jagora wanda ba wai kawai ya shafi tsarin rubuce-rubuce ne ba har ma da jan hankali kan amfani da fasahar rubuce-rubuce wajen samun kudade.

Ta kuma yaba wa babban editan kuma babban mataimakin shugaban kamfanin dillancin labarai na LEADERSHIP Ishiekwene bisa jajircewarsa da sanin ya kamata, wanda hakan ya taimaka matuka wajen ci gaban littafin.

Taron wanda ministan yada labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris ya jagoranta, ya samu halartar manyan mutane irin su Sanata Ireti Heebah Kingibe, da mawallafin jaridaer Vanguard Sam Amuka, da Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo, SAN, da tsohon kakakin shugaban kasa Dr. Reuben Abati, fitaccen marubucin jarida kuma mai gabatar da shirye-shiryen talabijin.

People are also reading