Home Back

Shugaban APC, Ganduje ya Raba ₦5.3m ga Wadanda Aka Kona a Harin Masallaci

legit.ng 2024/6/30
  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya raba kyautar N5.3m ga wadanda iftila'in harin masallaci ya rutsa da su
  • Wani matashi Shafi'u Abubakar ne ya kai hari kan masallacin garin Gadan dake karamar hukumar Gezawa inda akalla mutane 18 suka rasu zuwa yanzu
  • Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ya samu wakilcin shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya dauki alkawari sake gina masallacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano-Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya mika tallafin N5.3m ga wadanda iftila'in harin masallaci ya rutsa da su.

Matashi Shafi'u Abubakar mai shekaru 38 ne ya watsawa masallata fetur kana ya cinna musu wuta.

Abdullahi Ganduje
Shugaban APC Abdullahi Umar Ganduje ya raba tallafin kudi da abinci ga wadanda harin masallaci ya rutsa da su Hoto: @OfficialAPCNg Asali: Twitter

Nigerian Tribune ta wallafa cewa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 18 cikin 25 da suka kone, sauran na asibitin kwararru na Murtala suna karbar magani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 18 cikin 25 da suka kone.

Ganduje zai sake gina masallacin Gadan

Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya dauki alkawarin sake gina masallacin Gadan.

Mutane kimanin 25 ne suka kone a harin da aka kai musu suna tsaka da sallar asubahi.

Shugaban APC ya wakilci Ganduje

Shi ma masallacin ya kone, amma Abdullahi Ganduje ya ce zai gina shi ya koma sabo fil, kamar yadda New Telegraph ta wallafa.

A ziyarar da shugaban APC na Kano , Abdullahi Abbas ya kai a madadin Ganduje, an ba mutum bakwai da suka kone N7000.

Sannan an ba iyalan wadanda iftila'in ya rutsa da su N5m, tare da raba musu

'A dauki matakin shari'a Kan Shafi'u,' Atiku

A baya mun baku labarin cewa mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shawarci gwamnatin Kano kan matakin da ya kamata dauka kan Shafi'u Abubakar.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa kamata ya yi a gurfanar da shi gaban kotu tare da tabbatar da an hukunta shi idan an same shi da laifi.

Asali: Legit.ng

People are also reading