Home Back

Diomaye Faye ya samu goyon bayan Karim Wade a zaben Senegal

dw.com 2024/5/3
Dan takara Bassirou Diomaye Faye na dasawa da madagun adawa Ousmane Sonko
Dan takara Bassirou Diomaye Faye na dasawa da madagun adawa Ousmane Sonko

Wani jigo a siyasar Senegal Karim Wade ya yi kira ga magoya bayansa da su kada wa dan takarar adawa Bassirou Diomaye Faye kuri'a azaben shugaban kasar da zai gudana cikin kwanaki biyu masu zuwa. Wannan mataki na biyo bayan watsi da takarar dan tsohon shugaban kasa Wade na jam'iyyar PDS da kotun tsarin mulkin kasar ta yi saboda yana rike da paspo biyu a lokacin da ya gabatar da takara. Sai dai Karim Wade ya zargi dan takarar gwamnati Amadou Ba da marar hannu wajen hana masa takara.

'Yan takarar shugabancin kasar Senegal na gudanar da gangaminsu na karshe na yakin neman zabe. Jiga-jigan 'yan takara biyu da aka fi kyautata musu zato Amadou Ba da ke da kusanci da shugaba mai barin gado da Bassirou Diomaye Faye da ke dasawa da madagun adawa na gudanar da tarukansa na karshe ne a Dakar da kewaye kafin a dakatar da farfaganda da tsakar dare.

People are also reading