Home Back

Arangama ta barke a Kenya tsakanin 'yan sanda da matasa

dw.com 2024/7/3
Hoto: Monicah Mwangi/REUTERS

Arangama ta barke a Nairobi babban birnin kasar Kenya a Talatar nan, tsakanin 'yan sanda da matasa masu zanga-zangar nuna adawa da sabuwar dokar karin haraji da shugaba William Ruto ya gabatar, inda 'yan sandan suka rinka harba hayaki mai sa hawaye da kuma harsasan roba ga matasan.

'Yan sandan dai sun datse hanyar shiga majalisar dokokin kasar, wadda ke tafka muhawara kan kudurin karin harajin domin amincewa da shi.

Kuma tun a makon da ya gabata ne daruruwan matasan suka fantsama kan titunan Nairobi don nuna tirjiya da bijirewa wannan sabon tsari, da suka ce zai kara jefa al'ummar kasar cikin gararin rayuwa.

Yanzu haka dai masu zanga-zangar karya shingen jami'an tsaron, inda suka kutsa cikin zauren majalisar dokokin kasar, bayan da 'yan majalisar suka amince da dokar karin harajin.

People are also reading