Kun san yadda ake shiga jirgin ƙasan Abuja?
Kun san yadda ake shiga jirgin ƙasan Abuja?
Mintuna 11 da suka wuce
Mazauna Abuja na ci gaba da more zirga-zirga zuwa wasu sassan birnin a kyauta, a duk lokacin da suka hau sabon jirgin ƙasa mai sufuri a babban birnin na Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ne ya ƙaddamar da jirgin ƙasan a ƙarshen watan Mayu tun daga lokacin ne ya fara jigilar fasinjoji daga tsakiyar birnin Abuja zuwa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe.
Shugaban Najeriyar ya yi alƙawarin za a ci gaba da jigilar fasinjoji kyauta a jiragen ƙasan har zuwa ƙarshen wannan shekara.