Home Back

Zargin Almundahanar Biliyan ₦2.8b: EFCC Ta Gurfanar Da Hadi Sirika

leadership.ng 2024/7/6
Zargin Almundahanar Biliyan ₦2.8b: EFCC Ta Gurfanar Da Hadi Sirika

Alleged N2.8bn Fraud: EFCC Opens Case Against Sirika, Others

Zargin Almundahanar Biliyan ₦2.8b: EFCC Ta Gurfanar Da Hadi Sirika Gaban Kotu

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC, ta fara tuhumar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da wasu mutane uku, bisa zargin almundahanar Naira biliyan 2.6.

Sirika, tare da ɗiyar sa Fatima, Jalal Sule Hamma, da kuma Al-Duraq Investment Limited, suna fuskantar tuhume-tuhume guda shida da suka haɗa da zamba a ofis da kuma badaƙalar kwangila a babbar kotun birnin tarayya (FCT) dake Maitama.

Shaidu na farko na EFCC, Azubuike Okorie, tsohon ma’aikacin ma’aikatar sufurin jiragen sama, ya shaida rawar da ya taka a matsayinsa na Daraktan saye da sayarwa da kuma mataimaki na musamman ga Ministan, inda ya bayyana ayyukan sa na sa ido da tantance ayyuka, duk da cewa ba shi da hannu kai tsaye wajen bayar da kwangila.

Okorie ya bayyana cewa kwamitin aiwatar da ayyukan da ya jagoranta ya gano rashin jituwa a lokacin da ake sa ido kan ayyukan musamman a filin jirgin saman Katsina, inda babu wani ɗan kwangila da yake gudanar da aiki ciki har da Al-Duraq, duk da cewa akwai sunayensu matsayin ƴan kwangila.

Ya shaida cewar har ya kammala aikin gwamnati a watan Mayun 2023, ba a aiwatar da aikin kwangilar da kamfanin Al-Duraq ba wacce ta kai Naira miliyan 800. Ya ƙara da cewa, yana da masaniyar wani kuɗi da aka biya wa Al-Duraq kashi 30 cikin 100 na tara kuɗaɗen shiga, amma babu hannun shi cikin tsarin biyan kuɗi wanda aka yi shi bisa ƙa’ida ba.

Kanu Agabi, SAN, Lauyan Sirika, ya buƙaci da a ɗage zaman domin duba takardun ƙarar, buƙatar da wasu lauyoyin masu ƙara suka goyi bayan kuma masu gabatar da ƙara ba su yi hamayya ba.

Sakamakon haka, Mai shari’a Sylvanus Oriji ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 30 ga wata domin yi masa tambayoyi da kuma ci gaba da shari’ar.

People are also reading