Home Back

Yadda sama da mutum 100 sun arce daga Kurkukun Suleja, bayan ruwa da iska ya kwantar da katangar gidan

premiumtimesng.com 2024/5/5
Yadda sama da mutum 100 sun arce daga Kurkukun Suleja, bayan ruwa da iska ya kwantar da katangar gidan

Aƙalla ɗaurarru sama da 100 ne suka arce daga Gidan Kurkukun Suleja bayan ruwan sama mai ƙarfin gaske da kuma iska sun kwantar da wani ɓangaren katangar kurkukun Suleja, da ke Jihar Neja.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Laraba da dare, wajen ƙarfe 9 na dare.

Majiya ta ce ruwa da iska mai ƙarfi ya kayar da wani sashe na katangar, lamarin da ya bai wa ɗaurarru da dama samun damar tserewa.

Gidan Radiyon BBC ya ruwaito cewa a ɗaurarru 110 ne suka tsere. Amma dai wani mazaunin Suleja ya shaida cewa, “mun taimaka wa Jami’an Kula da Gidan Kurkuku, inda muka damƙa masu wasu mutum biyu da suka yi ƙoƙarin guduwa, amma muka damƙe su.”

An tabbatar da cewa an baza jam’i’an tsaro a Suleja da kewaye, domin ci gaba da farautar ɗaurarrun da suka arce.

Haka kuma an tsaurara matakan tsaro kan titin Suleja zuwa Minna, titin Suleja zuwa Kaduna, da kuma yankin cikin Madalla wato titin Minna zuwa Abuja.

Har lokacin buga wannan labarin ba a samu jin ta bakin Shugaban Kula da Gidajen Kurkukun Jihar Neja ba

People are also reading