Home Back

NLC, TUC Sun Aika Sabon Gargadi Ga Tinubu Kan Mafi Karancin Albashi

legit.ng 2024/7/1
  • An gargadi Bola Tinubu kan aikewa da sabon mafi karancin albashi ga majalisar tarayya ba tare da tuntubar kungiyar kwadago ba
  • Kungiyoyin NLC da TUC sun ce ya zama wajibi shugaban kasar ya tuntube su kafin ya mika dokar sabon albashin ga majalisar kasar
  • A cewar kungiyoyin, tuntubar wadanda ya dace kan sabon mafi karancin albashi zai haifar da daidaiton ma'aikata da gwamnati a kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Hadaddiyar kungiyar 'yan kwadago ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya tuntube ta kafin ya mika sabon mafi karancin albashi ga majalisar dokokin kasar.

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun ce hakan zai taimaka wajen kiyaye daidaiton ma'aikata da gwamnati a kasar.

An bukaci Bola Tinubu da ya tuntubi 'yan kwadago kafin ya aika sabon mafi karancin albashi ga majalisar tarayya
Mafi karancin albashi: NLC, TUC sun bukaci Tinubu ya nemi shawarwarin da ya dace. Hoto: @NLCHeadquarters, @officialABAT Asali: Twitter

Me yasa Tinubu zai tuntubi NLC, TUC?

Kungiyar kwadago ta ce za ta dage kan a biya mafi karancin albashin ma’aikata komai tsawon lokacin da za a dauka kafin a amince da sabon albashin, in ji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin NLC da TUC, Joe Ajaero da Festus Osifo ne suka bayyana haka a ranar Alhamis a gefen taron da kungiyar kwadago ta duniya ta shirya a birnin Geneva na kasar Switzerland.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta amince da N62,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi, yayin da kungiyar kwadago ta dage kan N250,000.

Bukatar ma'aikata kan mafi ƙarancin albashi

Da yake jawabi a taron hadin gwiwa, Ajaero ya bayyana cewa dole ne ma’aikata su bukaci a fara biyan mafi karancin albashi ba tare da la’akari da lokacin da majalisar tarayya ta zartar da dokar mafi sabon albashin ba.

Jaridar Tribune ta ruwaito Ajaero ya ce suna sa ran Tinubu zai gayyaci kwamitin bangarori uku zuwa wani taro domin tattauna yadda za a iya biyan albashi kafin a cimma matsaya.

Tinubu ya tsayar da mafi karancin albashi

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa Shugaba Tinubu ya sanar da kammala tattaunawa kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata da kuma kamfanoni masu zaman kansu.

Shugaban, a jawabinsa na ranar dimokuradiyya, ya ce nan ba da dadewa ba za a aika da wani kudurin dokar zartarwa ga majalisar tarayya domin sanya sabon mafi karancin albashi a cikin dokar Najeriya.

Asali: Legit.ng

People are also reading