Home Back

Ban yi kira da a tsige ko Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC ba – Gwamna Alia

premiumtimesng.com 2024/4/30
Ban yi kira da a tsige ko Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC ba – Gwamna Alia

Gwamna Hyacinth Alia na Benuwai ya musanta kiran zargin da ake yi wai ya yi kira ga shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Ganduje,ya yi murabus.

Wannan martani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa (CPS), Tersoo Kula ya fitar a ranar Laraba a Makurdi.

Hakan ya biyo bayan wasu rahotanni ne da ake yadawa a kafafen yada labarai cewa wai gwamnan ya yi kira da shugaban jam’iyyar ya yi murabas.

Kula ya ce babu wani lokaci da gwamnan ya nemi shugaban jam’iyyar APC na kasa ya yi murabus.

Ya ce gwamnan yana da kyakkyawar alaka da shugabancin Ganduje a APC.

” Gwamnan Benuwai na tare da Ganduje da kuma salon shugabancin sa. Bai taba furta kalami irin wanda ake yadawa a kafafen yada labarai na suka da shugabancin Ganduje ba.

People are also reading