Lauyoyin Nnamdi Kanu Sun Bukaci Ayi Gaggawan Fito da Shi, Sun Gabatar da Hujjoji
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Bayan shafe shekaru ana shari'a kan zargin Nnamdi Kanu, lauyoyinsa sun tura takarda ga gwamnati kan a sake shi.
Nnamdi Kanu ya kasance shugaban yan ta'adda masu fafutukar kafa kasar Biyafara a kudu maso gabashin Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lauyoyin Kanu sun tura takardar ne ga babban lauyan gwamnatin tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban lauyoyin Nnamdi Kanu, Barista Neameka Ejiafor ya ce sun tura takardar ne saboda kalaman da babban lauyan gwamnati ya yi.
Lauyan Kanu ya ce babban lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi ya ce bai da masaniya kan lamarin Kanu saboda haka suka rubuta masa takarda.
Lauyoyin sun ce suna fata idan ya karanta dalilan da suka nuna ya halasta a sake Nnamdi Kanu zai fahimta kuma ya ba da izinin sakinsa.
Ga abin da takardar ta kunsa:
"Mun rubuta takardar nan ne domin mu jawo hankalin ka kan abin da yake faruwa da Nnamdi Kanu."
"Mun tabbatar da cewa an boye gaskiyar lamarin ne daga gare ka saboda a hana ka tabbatar da adalci da kuma yin kira ga shugaban kasa Bola Tinubu ya ba da izinin sake Nnamdi Kanu."
Kanu ya kasance a tsare tun da aka kamo shi daga kasar Kenya a shekarar 2021, amma a cikin wasikar sun bayyana dalilai guda tara da suka nuna ya kamata a sake shi, rahoton Channels Television.
A wani rahoton, kun ji cewa ministan sufuri, Sanata Sa'idu Ahmed Alkali ya tabbatar da cewa jirgin kasan Legas zuwa Kano zai fara aiki.
Rahotanni sun nuna cewa Sanata Sa'idu Ahmed Alkali ya ce an sanar da fara aikin jirgin kasan ne bayan an masa gyare-gyare na musamman.
Asali: Legit.ng