Home Back

SHIRIN SAMAR DA ABINCI: Gwamnan Kano zai sayo wa manoman Kano takin zamani na Naira biliyan 5

premiumtimesng.com 2024/7/3
KANO: Gwamna Abba ya ce zai sa hannu kan hukuncin da kotu za ta yanke wa wanda ya cinna wa masallata wuta har 17 suka rasu

A ƙoƙarin da yake yi domin bunƙasa abinci wadatacce da inganta fannin noma, Gwamna Abba Kabir-Yusif na Jihar Kano ya amince a sayo takin zamani na Naira biliyan 5, domin samar wa manoman jihar.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna, Sanusi Dawakin Tofa ya fitar a ranar Talata, ya ce Gwamna ya amince a sayo takin a lokacin taron Majalisar Zartaswar Jihar Kano na 15, wanda ya gudana a Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Dama a lokacin kamfen na yaƙin nan zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, Gwamna Abba ya yi alƙawarin sayo taki domin rabawa ga ƙananan manoma a yankunan karkara, saboda su samu yalwa da albarkar noma a daminar 2024.

A kan haka ne Majalisar Zartaswar Jihar Kano ta amince a ware Naira 5,073,840,00, domin sayen takin zamani a raba a ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar.

A ranar Asabar ce aka amince da wannan ƙudirin a taron Majalisar Zartaswa da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Da kuma ya ke nuna damuwa dangane da masifar tsadar kayan abinci, Abba ya sayo kayan abinci na biliyoyin nairori ya raba wa marasa galihu, domin rage masu raɗaɗin tsadar rayuwa a jihar.

“Wannan takin zamani da za a sayo, zai zama kamar wata ribar-ƙafa ce, domin dama Kamfanin Haɗa Kayan Noma na KASCO ya samar da takin zamani, wanda duk za a haɗa a sayar wa manoma a farashi wanda gwamnati za ta yi mai rahusa, a matsayin tallafi na gudummawar ta wajen bunƙasa harkokin noma da samar da abinci a Jihar Kano.”

People are also reading