Home Back

Gwamnatin Tinubu Ta Dauki Mataki Yayin da Kungiyoyin Kwadago Ke Shirin Fara Yajin Aiki

legit.ng 2024/6/29
  • Gwamnatin tarayya a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta roƙi alfarma a wajen shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC
  • Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Idris Mohammed ya yi kira ga ƙungiyoyin ƙwadago da su ƙara baiwa shugaban ƙasa lokaci
  • Idris Mohammed ya yi wannan roƙo ne bayan ƙungiyar NLC ta sanar da shirinta na fara yajin aikin sai baba ta gani tare da ƙin amincewa da tayin mafi ƙarancin albashi na N60,000 da gwamnatin tarayya ta yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta roƙi ƙungiyoyin ƙwadago kan shirinsu na shiga yajin aiki.

Gwamnatin ta buƙaci da su sake duba matakin da suka ɗauka na shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Litinin, 3 ga watan Yuni 2024.

Gwamnatin tarayya ta roki kungiyoyin kwadago
Gwamnatin tarayya ta bukaci kingiyoyin kwadago su hakura da shiga yajin aiki Hoto: Nigeria Labour Congress HQ, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Ƴan ƙwadago za su shiga yajin aiki

Idan dai za a iya tunawa, shugabannin ƙungiyar ƙwadago na NLC da TUC sun ayyana yajin aikin sai baba ta gani a faɗin ƙasar nan a ranar Juma’a 31 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙungiyar NLC, Kwamared Joe Ajaero, ya ce sun yanke shawarar shiga yajin aikin ne saboda gazawar gwamnatin tarayya na ƙara mafi ƙarancin albashi daga N60,000 tare da cire ƙarin farashin wutar lantarki.

Wane roƙo gwamnatin tarayya ta yi?

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa Idris Mohammed yayin wata ta musamman da jaridar The Punch ya buƙaci ƴan ƙwadagon da su haƙura da shiga yajin aikin.

Ministan ya bayyana cewa yajin aikin ba shine mafita ba kan tattaunawar da ake yi dangane sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata.

Saboda haka sai ministan a madadin gwamnatin tarayya ya roƙi ƙungiyoyin ƙwadagon da su ɗage yajin aikin da suke shirin yi.

"Gwamnati tana roƙon ƙungiyoyin ƙwadago da su sake duba matsayarsu. Gwamnatin tarayya ta bayar da tayin Naira 60,000, kuma duk abin da gwamnati za ta yi, za ta yi ne saboda ƴan Najeriya."
"Ba za mu so yin wani abu da zai jefa ƙasar nan cikin wata matsala ba."

- Idris Mohammed

Ƴan ƙwadago sun sassauta buƙatunsu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar kwadago ta TUC ta ce da yiwuwar za su sauko daga N494,000 da suke buƙata a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan ƴan kwadagon sun rage yawan kuɗin da suke buƙata a matsayin mafi ƙarancin albashi daga N497,000 zuwa N494,000.

Asali: Legit.ng

People are also reading