Home Back

NLC: Minista Ya Yi Magana Kan Sabon Mafi Karancin Albashi Bayan Ya Gana da Tinubu

legit.ng 2024/7/3
  • Bola Ahmed Tinubu ya gana da ministoci biyu game da batun sabon mafi ƙarancin albashi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
  • Gwamnatin tarayya na ci gaɓa da tattauna da ƴan kwadago da nufin cimma matsaya bayan sun janye yajin aikin da suka fara
  • Sai dai duk da gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin ƙara yawan tayin da ta yi daga N60,000, har yanzu babu wanda ya san adadin da za ta gabatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Yayin da tawagar gwamnatin tarayya da ƴan kwadago ke ƙoƙarin cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi, ministan kuɗi, Wale Edun ya gana da Bola Tinubu.

Ministan ya bayyana cewa babu wani abun tayar da hankali game da sabon albashin ma'aikata saboda haka kowa ya kwantar da hankalinsa.

Bola Tinubu da Wale Edun.
Ministan Kudi Wale Edun ya ce babu wani abun damuwa kan sabon mafi ƙarancin albashi Hoto: @Kukoyibusola @Mario9jaa Asali: Twitter

Edun ya yi wannna furucin ne jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Villa ranar Alhamis, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake zantawa da ƴan jarida masu ɗauko rahoto a gidan gwamnati, Edun ya buƙaci ƴan Najeeiya su kwantar da hankulansu, kar su damu.

Ministan kuɗi da harkokin tattalin arziƙin ya gana da shugaban ƙasa ne ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni tare da ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Atiku Bagudu.

Duk da bai yi cikakken bayani kan ajendar wannan zama ba, ana hasashen ba zai rasa nasaba da batun mafi ƙarancin albashi ba, kamar yadda Channels tv ta kawo.

Edun ya miƙa lissafin albashi ga Tinubu

Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa Wale Edun ya miƙa lissafin sabon mafi ƙarancin albashi ga Bola Tinubu.

Ministan ya yi haka ne bayan Tinubu ya ba shi wa'adin sa'o' 48 ya kawo masa lissafin yadda za a aiwatar da sabon albashin.

Gwamnatin Tinubu ta gana da NLC

A wani rahoton kun ji cewa an tashi ba tare da cimma matsaya ba a tattaunawar wakilan ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnatin tarayya kan mafi ƙarancin albashi.

Hakan ya faru ne bayan gwamnatin tarayya ta gaza yin sabon tayi kan abin da za ta riƙa biya a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

Asali: Legit.ng

People are also reading