NLC: Minista Ya Yi Magana Kan Sabon Mafi Karancin Albashi Bayan Ya Gana da Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Yayin da tawagar gwamnatin tarayya da ƴan kwadago ke ƙoƙarin cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi, ministan kuɗi, Wale Edun ya gana da Bola Tinubu.
Ministan ya bayyana cewa babu wani abun tayar da hankali game da sabon albashin ma'aikata saboda haka kowa ya kwantar da hankalinsa.
Edun ya yi wannna furucin ne jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Villa ranar Alhamis, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake zantawa da ƴan jarida masu ɗauko rahoto a gidan gwamnati, Edun ya buƙaci ƴan Najeeiya su kwantar da hankulansu, kar su damu.
Ministan kuɗi da harkokin tattalin arziƙin ya gana da shugaban ƙasa ne ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni tare da ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Atiku Bagudu.
Duk da bai yi cikakken bayani kan ajendar wannan zama ba, ana hasashen ba zai rasa nasaba da batun mafi ƙarancin albashi ba, kamar yadda Channels tv ta kawo.
Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa Wale Edun ya miƙa lissafin sabon mafi ƙarancin albashi ga Bola Tinubu.
Ministan ya yi haka ne bayan Tinubu ya ba shi wa'adin sa'o' 48 ya kawo masa lissafin yadda za a aiwatar da sabon albashin.
A wani rahoton kun ji cewa an tashi ba tare da cimma matsaya ba a tattaunawar wakilan ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnatin tarayya kan mafi ƙarancin albashi.
Hakan ya faru ne bayan gwamnatin tarayya ta gaza yin sabon tayi kan abin da za ta riƙa biya a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.
Asali: Legit.ng