Home Back

‘Yan Nijeriya A Hannun Tinubu Cikin Shekara Guda

leadership.ng 2024/6/18
Tinubu
  • Ba Mu Cire Rai Ba Har Yanzu – Farfesa Bello
  • Matakansa Sun Fi Dadada Wa Kasashen Waje – Masani
  • A Kara Juriya – Gwamnati
  • ‘Yan Nijeriya Na Shan Wahala – ACF

A ‘yan kwanakin nan ne Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ke cika shekara daya a kan karagar mulki, bayan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayun 2023.

A cikin shekara guda daya tal, shugaban kasar ya zo da manufofi da suka shafi rayuwar ‘Yan Nijeriya tare da yin tasiri kala-kala musamman ta fuskar tattalin arziki.

‘Yan Nijeriya suna ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi da ba a taba gani ba tun shekara 64 da suka wuce lokacin da Nijeriya ta samu ‘yancin kai daga turawa.

Tun a ranar 29 ga watan Mayu 2023 yayin da aka ranstar da shi a matsayin Shugaban Kasa, Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur, wadda ta zama silar kusan dukkan hauhawar farashin da ake ci gaba da fuskanta a dukkan harkokin rayuwar al’ummar Nijeriya, inda talakawa suka fi dandana kudarsu.

A karshen mulkin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari hauhawar farashi ba ta wuce kashi 22.41, farashin kayan abinci da kayan masarufi kuma yana kashi 24.82, amma daga bisani kayan abainci kamar man gyada da man ja, doya, wake masara, shinkafa duk sun yi tashin gwauron zabo. A yau, hauhawar farashin ta karu zuwa kashi 33.20, farashin buhun shinkafa ya tashi daga N28,000 a farkon mulkin Tinubu zuwa N90,000 a musamman a wata uku da suka wuce, kodayake a halin yanzu ana samun shinkafar a kan N65,000 a wasu wurare.

Haka kuma, wutar lantarki wadda ita ce kashin bayan duk wani ci gaban masana’antu da tattalin arzikin kaasa, a da yana N68 a kan kilowatt amma a halin yanzu gwamnati Tinubu ta mayar da shi N225. Wannan matakin ya yi sanadiyyar durkushewar manya da kananan masana’antu da dama a sassan kasar nan. A wananan lokaci ne kuma aka samu manyan kamfanoni da dama suka tattara ina su ina su suka fice daga kasar nan sakamakon tsare-tsare da manufofi da dama na gwamnati wanda yake kawo musu tarnaki ga ci gabansu. Wasu daga cikin kamfanonin sun hada da Netsle, Shoprite da sauransu.

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa, karin kudin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi ya haifar da hauhawar farashin kayan amfanin yau da kullum, misali a watan Mayu na shekarar 2023, ana sayar da buhun siminti mai nauyin kilogram 50 a kan N3000 amma a yanzu duk da kokarin gwamnatin tarayya da daidaita farashi, siminti yana kaiwa a tsakanin N8000 da N9000 har kuma ya kai zuwa N13,500 a watan Fabrairu na wannan shekarar 2024.

Masu lura da al’murran yau da kullum sun dora alhakin wannan tashin farashin a kan tsare-tsaren tattalin arzikin wannan gwamnatin. Idan za a iya tunawa, a shekarar 2023 kungiyar masu sarrafa siminti ta ja hankalin gwamnati a kan shirin fara amfani da siminti wajen gina hanyoyi, tabbas, gashi kuwa a yau farashin buhun siminti ya kai N9,000 daga N3000 a karshen mulkin Buhari.

A bangaren farashin dala kuma, lamarin sai a hankali, idan aka kwatanta da yadda farashin yake a watan Mayu na 2023 inda ake samun dala a kan 460.702 (USD/NGN), amma a yau ana samun dala ce a kan N1,450.

Wannan tare da karin kudin man fetur ya haifar wa da al’ummar Nijeriya fiye da miliyan 135 matsaloli musamman talakawa. Tallafin da gwamnati ke yekuwar tana bayarwa sakamakon janye tallafin man fetur duk suna komawa ne ga ‘yan siyasa da ‘yan kanzaginsu.

A gaskiya, Shugaba Tinubu, bai bayyana wa al’umma Nijeriya cikakkun manufofinsa na tattalinh arziki ba a lokacin da yake yakin neman zabe, in ban da alkawarin da ya yi na janye tallafin man fetur, wannan ma sakamakon shinfidar da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ne musamman yadda ake neman a kauce wa halin cin bashi wajen tafiyar da harkokin gwamnati, a kan haka wasu masana suka yi maraba da batun cire tattalifin man fetur amma ba su yi hasashen matsalolin da lamarin zai haifar ba, musamman yadda jami’an gwamnati da aka dora wa alhakin raba tallafin rage radadin janye tallafin fetur su ne kuma suka kasance a gaba wajen wawushe abin da ya kamata su raba wa al’umma.

Wani abin takaici na wannan gwamnatin a cikin shekara daya shi ne yadda ta rungumi tsarin gwamanatin Buhari na cin bashi daga kasashen waje. A kasafin kudinsa na farko, ya bayar da muhimmanci ne ga sayen kayan alatu wadanda ba su da nasaba da bunkasa tattalin arziki da rayuwar al’umma. Kasafin kudin ya fi mayar da hankali wajen ware Naira Biliyan 1.9 wajen saya wa matar shugaban kasa motoci na alfarma.

Haka kuma gwamnatin Tinubu ta ware Naira biliyan 2.9 domin canza motocin alfarma na fadar shugaban kasa da kuma yi wa wani sashi na fadar shugaban kasa da ofishin mataimakinsa kwaskwarima.

Kasafin kudin ya yi tanade-tanaden ayyuka da dama na samar da jin dadi ga manyan jami’an gwamnati da suka hada da samar da motocin hawa, gyara ofishoshi da gidajen kwanansu. Wannan ya sanya masana na korafin cewa, gwamnatin Tinubu ta fi daukar manyan jami’an gwamnati da muhimmanci fiye da taimaka wa rayuwar talakawa wadanda su ne suka yi tururuwa wajen kada masa kuri’a a yayin zabe.

Cikin misalai na irin wannan matakai na Shugaba Tinubu shi ne yadda aka ware makudan kudade domin sayen motocin alfarma ga ‘yan majalisar kasa da kuma irin kudade da aka ware musu domin gudanar da aiki.

Ana cikin matsi da tsadar rayuwa sai ga shi kuma gwamnatin ta sanar da karin kudin wutar lantarki da kashi 250 bisa 100, wanann ma ya sa masana ke ganin tamkar Tinunu bai san halin da al’umma ke ciki a Nijeriya ba.

Nan take kungiyoyin kwadago da masu rajin kare hakkin al’umma suka nuna rashin amincewarsu. Ba a gama fita daga firgicin karin kudin wutar lantarki ba sai gashi an wayi gari da wani sabon haraji, wai na tsaron intanet, kodayake an dakatar daga bisani, amma a karkashinsa, Babban Bankin Nijeriya CBN ya umarci bankuna su rika cire daga kashi 7.5 zuwa kashi 10 a kan kudaden da masu hulda da bankuna ke hada-hadarsu. A cewar CBN, ana son a yi amfani da kudaden ne don yaki da masu zamba ta intanet tare da tabbatar da tsaron intanet (Cybersecurity), wasu masana na ganin gwamnati na neman kudade ne ta kowacce hanya domin ta biya basukan da take lodawa a kullum tana kuma son kauce wa nauyin da tsarin mulki ya dora mata na kare rayuwa da dukiyar al’umma.

Idan har ana son duba tasirin shugaban kasa a kan mulki na tsawon shekara 1 dole a duba sassa daban-daban da suka hada da tattalin arziki, jin dadin jama’a, aikin gwamnati da kuma yadda al’umma ke tunani da fata a kan gwamnatin.

A tsokancisa a kan yadda al’umma ke kallon matakan tattalin arziki na Shugaba Tinubu, shugaban kamfanin AntHill Concept Limited wanda manba ne a hukumar gudanarwar daya daga cikin jaridunmu ta NATIONAL ECONOMY, Dakta Emeka Okengwu, ya ce, yayin da matakan tattalin arzikin Tinubu ke takura ‘yan Nijeriya, al’ummar kasashen waje da cibiyoyin kudi na waje suna matukar yaba wa matakan.

Idan za a iya tunawa, Asusun Ba Da Lamuni Na Duniya (IMF) ya karfafa batun cire tallafin man fetur da na wutar lantarki, wai yin haka ne hanyar tabbatar da bunkasar tattalin arzikin duniya. Haka ma Bankin Duniya ya nuna amincewarsa ga sauye-sauyen tattalin arzikin Shugaba Tinubu. “Na yi imanin cewa nan gaba kadan za a ci gajiyar wadannan matakai na Tinubu,’ in ji shi.

Haka kuma wani masanin tattalin arziki mai suna, Moses Igbrude, ya bayyana cewa, matakan tattalin arzikin Tinubu na da kyau amma suna daukar lokaci kafin talaka ya gani a kasa, ya nemi a kara samar da tallafi ga talakawa, a kuma sanya ido domin ka da a karkatar da tallafin kamar yadda ya faru a lokutan baya.

A nasa tsokacin, wani malami a Jami’ar Adeleke ta Jihar Osun, Farfesa Tayo Bello, ya bayyana cewa, matakan tattalin arzikin Shugaba Tinubu suna da muhimmanci amma saboda al’umma ba su saba da su ba shi ya sa a ke tsoronsu kuma ga shi suna haifar da matsin rayuwa, ya ce, ya kamata gwamnati ta tabbatar da cewa, al’umma sun amfana da tsare tsaren a nan gaba. Ya kuma nemi jami’an gwamnati su rika gudanar da abubuwansu a bayyana ba tare da boye-boye ba, ta haka al’umma za su yardar da cewa, ba su kadai ke sadakauwar ba.

Ya kuma lura da cewa, gwamnatin tarayya ta yi alkawarin amfani da kudaden da aka samu daga janye tallafin fetur wajen bunkasa rayuwar al’umma da samar musu ababen more rayuwa, to ya kamata a gani a kasa.

Shi kuwa Dakta Tuniji Olaleye, malami a Jami’ar Jihar Legas ya nemi gwamnati ce ta bayar da karfi wajen samar wa al’umma ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya, makarantu, gidaje masu saukin kudi da tallafi ga talakawa marasa karfi.

Ya kuma bukaci kungiyoyin fararen hula su sa ido a kan yadda ake kashe kudin gwamanati da irin yadda ake aiwatar da wasu manufofi. Ta haka jami’an gwamnati za su tsayu wajen aiki tukuru domin tsoron ka da a fallasa su, ita kuma gwamnati ta tabbatar da ana hukunta duk wanda aka kama da laifin sama da fadi da kayan al’umma.

Ya bayar da misalin Ministar Jin Kai, Betta Edu da aka kama da zargin sace dukiyar gwamnati da aka ware domin tallafa wa al’umma amma har yanzu ba a san halin da ake ciki ba game da hukunta ta ba.

Haka kuma wani masanin tattaalin arziki mai suna Dakta Samuel Jakpor, ya ce, ‘Yan Nijeriya za su dora shirye-shiryen tattalin arzikin Shugaba Tinibu a sikelin yadda rayuwarsu ya bunkasa ko akasin haka, musamman abin da ya shafi rashin aiki yi ga matasa, hauhawar farashi, shigowar masu zuba jari daga kasashen waje.

Ya kara da cewa ana auna ci gaban tattalin arziki ne da irin ci gaban da al’umma ke samu, in har ana shan wahala, tattalin arziki kuma ya ki bunkasa ba yadda za a yarda cewa, ana samun ci gaba. “Zuwa yanzu wannan gamnatin ba ta yi abin da al’umma za su yaba ba, amma lokaci ne kawai zai tabbatar mana da yadda abubuwa za su kasance, muna dai fatan a samu sauki,” in ji shi.

A nata martanin game da manufofin tattalin arziki na Shugaba Tinubu, Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta bayyana cewa, ‘Yan Nijeriya da dama na cikin matsalar tattalin arziki sakamakon tsare-tsaren da aka bijiro da su a cikin shekara 1 na shugabancin Tinubu.

Bayanin haka yana kunshe ne a takardar manema labarai da babban sakataren kungiyar, Farfesa Muhammad Tukur Baba, ya Sanya wa hannu a Kaduna.

Sanarwa ta ce, a kullum ‘yan Nijeriya na kara shiga mastala sakamakon hauhawar farashi, rashin aikin yi da kuma tabarbarewar harkokin rayuwa.

Kungiyar ta ce, gwamnati ce ta haifar da dukkan mastalolin da ake fuskanta ta hanyar rashin samar da tsarin da zai rage wa al’umma radadin da suke shiga sakamakon tsare-tsaren tattalin arzikin wannan gwamnatin.
A kan haka, ACF ta bukaci gwamnati a dukkan matakai ta samar da mafita don farfado da rayuwar al’umma da gaggawa.

Ta kuma yi tir da kare-karen haraji da ake yi wa ‘yan Nijeriya, “Hakan zai kara mastala ne ga ‘Yan Nijeriya”, in ji ta.
A bangaren gwamnatin tarayya kuwa, mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa, dukkan manufofin da suke bullo da su, abubuwa ne da suka yi daidai da bukatar Nijeriya kuma su ne mafi alfanu ga Nijeriya a halin yanzu.

Ya yi wannan bayanin ne a taron duba ayyukan da Shugaba Tinubu ya yi a cikin shekara daya da aka yi wa lakabi da “Asiwaju Score Card Series” a Abuja.

Ya ce, kowacce kasa na da nata tarihi da matsalolin da take fuskanta, a kan haka, “Za mu tsayu a kan gabatar da abin da muka tabbatar shi ne mafi alfanu ga Nijeriya da ‘yan Nijeriya.”

Shettima, wanda babban jami’i a ofishinsa, Dakta Aliyu Modibbo, ya wakilta ya ce, matakai 8 da Tinubu ya bullo da su sun bayar da cikakkiyar mafita ga matsalar tattalin arzikin kasa, domin gwamnatinsu ta zuba jari mai yawa a bangaren aikin gona, masana’antu da sauransu, wanda hakan ya rage dogaron da Nijeriya ke yi ga shigo da kayayyakin abinci, ya kuma karfafa sarrafa kayayyaki a cikin gida.

A kan haka ya nemi al’umma su kara hakuri, ‘Nan gaba kadan komai zai daidatu’, in ji shi.

People are also reading