Abin da ya kamata ku sani na ladubban Sallar Layya
Abin da ya kamata ku sani na ladubban Sallar Layya
Mintuna 7 da suka wuce
Sheikh Mu'azzam Sulaiman Khalid, malamin addinin Musulunci a Kano ya yi mana ƙarin haske a kan ladubban Sallar Layya da suka kamata ku sani, yayin da kuke shagulgulan wannan babbar rana ta Idi.
Malamin addinin ya ce bai kamata a ajiye naman layya ya wuce tsawon kwanakin shagulgulan sallar ba.
Ya ƙara da cewa na daga cikin ladubban Sallar Layya a halarci Idi, sannan da zarar an sauko to a gaggauta yanka dabbar layya.
Kuma idan za a yi yankan to a kyautata niyya, ta hanyar ƙudurce niyyar neman kusancin ubangiji ta hanyar yin hakan.