Home Back

Julian Nagelsmann: Kocin Jamus ya tsawaita kwataraginsa zuwa 2026

bbc.com 2024/5/5
A

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Jamus Julian Nagelsmann ya sanya hannu kan sabuwar kwataragi tsakaninsa da Jamus da za ta kai shi zuwa 2026 bayan an kammala Kofin Duniya.

An naɗa Nagelsmann mai shekara 36 a matsayin wanda ya maye gurbin Hansi Flick a watan Satumbar 2023 ya kuma yi nasara a wasa uku cikin shida da ya ja ragama.

Kwantaragin da ya fara sanyawa hannu tsakaninsa da Jamus za ta ƙare ne watan Yuli bayan an kammala Euro 2024 da Jamus za ta karɓi baƙunci.

"Wannan hukunci ne da na ɗauka da gaske. Ba ƙaramar girmamawa ba ce ka jagiranci tawagar ƙasa," in ji Nagelsmann.

Har yanzu ba a fara wasannin neman gurbin Kofin Duniya wanda ƙasashen Amurk da Canada da Mexico za su hada hannu wajen karɓar bakuncin gasar.

Tun daga 2016, Jamus ba ta samu damar tsallake zagayen 'yan 16 ba a manyan gasanni, an cire ta daga Kofin Duniya biyu na baya a matakin rukuni, sannan aka cire ta a zagayen farko na sili daya kwale na Yuro 2020 da Ingila ta ɗauki nauyi.

Ta samu kanta cikin rukunin Scotland da Hungry d Switzerland a gasar Euro 2024.

Ana jita-jitar kocin zai iya komawa Bayer Munich domin maye gurbin Thomas Tuchel da zai bar ƙungiyar a ƙarshen wannan kakar.

People are also reading