Home Back

Gwamnatin Tarayya Ta Gano Mutane 9, ‘Yan Canjin Kudi 6 Masu Tallafawa Ta’addanci A Nijeriya

leadership.ng 2024/5/3
Gwamnatin Tarayya Ta Gano Mutane 9, ‘Yan Canjin Kudi 6 Masu Tallafawa Ta’addanci A Nijeriya 

Gwamnatin Tarayya ta ce ta gano wasu mutane da kamfanoni 15 da suka hada da daidaikun mutane 9 da wasu kamfanoni 6 na ‘yan canjin kudi (BDC), wadanda ake zargi da hannu wajen bada kudade don taimakawa ta’addanci.

Sashin Leken Asiri na Kuɗi ya ba da cikakkun bayanai game da wannan binciken ta hanyar daftarin aiki mai taken “Zayyana daidaikun mutane da ƙungiyoyi a Maris 18, 2024.”

Takardar ta bayyana cewa, kwamitin kakaba takunkumi na Nijeriya ya yi zama a ranar 18 ga Maris, 2024, inda aka ba da shawarar kakabawa wasu daidaikun mutane da kamfanoni takunkumi biyo bayan samunsu da hannu dumu-dumu wajen bayar da kudade don tallafawa ta’addanci.

Daga cikin mutanen da aka ambata a cikin takardar, akwai wani mawallafin jarida da ke zaune a Kaduna, Tukur Mamu, wanda a halin yanzu haka ke hannun gwamnatin tarayya kan zarginsa da taimakawa ‘yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna a watan Maris din 2022.

People are also reading