Home Back

Yadda Ƙungiyar Matasan Arewa Kan Harkokin Tsaro Ta Shirya Tattaunawa Kan Batun ‘Yansandan Jihohi

leadership.ng 2024/6/26
Yadda Ƙungiyar Matasan Arewa Kan Harkokin Tsaro Ta Shirya Tattaunawa Kan Batun ‘Yansandan Jihohi

Kungiyar Matasan Nijeriya Kan Harkokin Tsaro (CONYSSA), ta shirya taron masu ruwa da tsaki na ƙasa; domin tattaunawa a kan shawawarin da ake yi game da samar da ‘yansandan jiha a faɗin jihohi 36 na tarayya wanda aka gudanar a Cibiyar Bunƙasa Al’amuran Sojoji da ke Abuja (Army Resource Centre).

Da yake yin nasa wajibin a wajen taron da aka shirya tare da haɗin gwiwar Rundunar ‘Yansandan Nijeriya, Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Dakta Isa Yuguda ya yi tsokaci kan cewa, wajibi ne a zurfafa bincike a kan ƙalubalen da ke fuskantar jami’an ‘yansanda da sauran jami’an tsaron wannan ƙasa, matuƙar ana so su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

Yuguda ya ƙara da cewa, a matsayin Nijeriya ta ƙasa; dole ne ta ƙara ƙaimi wajen sanin matsalolin da ke addabar waɗannan jami’ai, kafin ta kai ga cimma nasarar da take buƙata a tsakaninsu.

Ya ƙara jaddada cewa, “ƙasar da take da ingantaccen tsaro, ita ce wadda zuba jari ke matuƙar bunƙasa a cikinta. Don haka, kafin Nijeriya ta kai ga matsayin da ake buƙata a fannin tsaro, dole ne ta sake jajircewa tare da samun mutane masu matuƙar kishi, ɗa’a, ƙwarewa, aikin yi da kuma adalci a tsakanin al’umma.

Tsaro

Har ila yau, tsohon gwamnan; ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga sauran al’ummar ƙasa, domin su farka tare da kasancewa cikin shiri; don sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tallafa wa gwamnati tsakaninsu da Allah, domin ganin an samu ci gaban ƙasa.

Kazalika, ya buƙaci mahalarta wannan taro da a koda-yaushe su riƙa tunanin samar da mafita tare da ci gaban ƙasar baki-ɗaya.
Ya ci gaba da cewa, “Muna buƙatar gyara ‘yansandanmu, domin abin tambaya shi ne; shin sun samu horo mai kyau, suna samun albashi mai kyau, suna da ingantattatun kayan aiki, suna samun horon da ya kamata ɗansanda ya samu ko kuma a’a kawai abin da ake cewa; muna ɗansanda ne?
Saboda haka, “Wajibi ne mu fara magance matsalolin da suka shafi ‘yansanda, maimakon ƙirƙirar wasu ‘yansandan waɗanda za su iya zama haɗari ko barazana da makamai a hannunsu.”

Haka zalika, shi ma a nasa tsokacin; Mai Martaba Cif Ayini Clement, wanda yake da ra’ayin samar da waɗannan ‘yansanda na jihohi ya bayyana cewa, akwai buƙatar a ƙara wa ‘yansandan tarayya ƙwarin gwiwa, domin samun damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Tsaro

Cif ya ƙara da cewa, fa’idar samar da ‘yansandan jihohi ita ce, duk yankin da aka ɗauki ɗansanda aiki; ya san lungu da saƙo na wannan waje tare da dukkanin al’ummar da ke zaune a yankin.

Haka zalika, shi ma Darakta Janar mai kula da harkokin tsaro da binciken shari’a a Nijeriya, Dakta Okocha Morgan; ya yi kira ga gwamnati da ta taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi tare da sake fasalin harkokin tsaro a Nijeriya, wanda ya haɗa da horar da ma’aikata da kuma ɗaukar wasu ƙwararrun ma’aikatan.

Bugu da ƙari, tun da farko; Darakta Janar na wannan ƙungiya ta Haɗin Kan Matasan Nijeriya Kan Harkokin Tsaro (CONYSA), Ambasada Ade Emmanuel ya ce, manufar wannan taro shi ne; tattaunawa a kan muhimmanci ko rashin muhimmancin samar da ‘yansandan jihohi da ake ta faman taƙaddama a kansa.

“Babu shakka, matasa na da gudunmawar da za su iya bayarwa; domin yaƙi da rashin tsaro matuƙar an yi amfani da su yadda ya dace, sannan ‘yansandan jihohi na iya samun ci gaba a wasu ƙasashen da suka ci gaba; suke da kuma kishin ƙasa fiye da mu, amma aiwatar da shi a nan ko shakka babu; na iya haifar da mummunan rikici.

Saboda haka, “ya kamata gwamnatocin jihohi su yi aiki yadda ya kamata da ‘yansandan tarayya, domin samun sauƙi, inganci da kuma ɗorewar zaman lafiya a faɗin wannan ƙasa baki-ɗaya.

Har ila yau, taron ya samu halartar wakilan hukumomin soja da na jami’an tsaro daban-daban a Nijeriya da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

People are also reading