Home Back

Hukumar Gandun Daji ta babbake gonar tabar wiwi mai faɗin kadada 20

premiumtimesng.com 2024/4/29
Hukumar Gandun Daji ta babbake gonar tabar wiwi mai faɗin kadada 20

A wani ƙoƙarin kawar da shaye-shaye da tu’ammali da muggan ƙwayoyi, Gwamnatin Jihar Ekiti ta banka wuta kan wata makekiyar gonar rainon dashen ƙananan ganyen tabar wiwi mai faɗin hekta 20.

Sakataren Hukumar Kula da Gandun Dajin Jihar Ekiti me ya bayyana cewa an ƙone ganyen tabar wiwi ɗin ne a cikin Gandun Dajin Ise.

Ya ce jami’an kula da Gandun Daji ne suka banka wa makekiyar gonar wuta.

Gwamnatin Jihar Ekiti ta ce ta na nan kan bakan ta na maida himma sosai wajen daƙile duk wasu haramtattun ayyuka musamman a cikin dazukan jihar, a bisa ƙudirin ta magance handamar gandun daji a ke yi.

Babban Sakataren Hukumar Kula da Gandun Daji ta Jihar Ekiti, Sunday Adekunle ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, a Ado Ekiti, babban birnin jihar.

Ya ce an samu nasarar babbake ganyen tabar wiwi ɗin bayan labarin da aka kwarmata cewa akwai wasu ɓatagari na gudanar da laifuka sosai a cikin Gandun Dajin Ise.

Ya ce dama ɗaya daga cikin ajandojin hukumar ce ta tabbatar ta yi wa duk wani ɓatagari hayaƙin da zai fitar da shi daga dajin ɗungurugum.

 
People are also reading