Sallah: Bayan Sanata Yari, Ɗan Majalisa Ya Ba Ƴan Mazaba Raguna 300, N250m a Zamfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Dan Majalisar Tarayya a jihar Zamfara, Hon. Aminu Jaji ya raba raguna 300 saboda bukukuwan sallah.
Jaji ya raba ragunan ne ga mambobin jam'iyyar APC da shugabanninsu da kuma marasa karfi a mazaɓarsa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugabanni kwamitin gudanarwar dan Majalisar, Aliyu Abubakar ya fitar, cewar The Guardian.
Aliyu ya ce Jaji ya kuma raba N250m ga ƴan mazabar da sauran marayu da marasa karfi domin yin bukukuwan sallah.
"Wannan kyautatawa ce ta shekara wanda ya ware domin mambobin APC da sauran jama'a domin yin walwala a sallah."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Wadanda za su ci gajiyar sun hada da shugabanni jam'iyyar a matakin jiha da kananan hukumomi da unguwanni."
"Sannan sauran sun hada da dattawan jam'iyyar APC da tsofaffin wadanda suka rike mukaman siyasa."
- Abubakar Aliyu
Ɗan Majalisar shi ke wakiltar mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji a jihar Zamfara karkashin jam'iyyar APC.
Karin bayani na tafe ....
Asali: Legit.ng