Home Back

Ana Tsaka da Rikicin Sarauta, Ganduje Ya Yi Babban Rashi a Jihar Kano

legit.ng 2024/7/2
  • Allah ya yiwa surukar Ganduje, Hajiya Asiya Muhammada Gauyama rasuwa da safiyar ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024
  • Ofishin shugaban APC na kasa ya sanar da cewa za a yi janazar Hajiya Asiya, mahaifiyar Gwaggo a gidan Ganduje da ke Kano da misalin karfe 2:00 na rana
  • Wannan na zuwa ne kwanaki ɗaya bayan rasuwar surukar mstaimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima

Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Dokta Abdullahi.Umar Ganduje ya yi babban rashi a jihar Kano.

Surukar Ganduje, Hajiya Asiya Muhammad Gauyama, ta riga mu gidan gaskiya da sanyin safiyar yau Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024.

Abdullahi Umar Ganduje.
Surukar Ganduje, Hajiya Asiya ta riga mu gidan gaskiya a Kano Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje Asali: Twitter

Mai magana da yawun shugaban APC na ƙasa, Edwin Olofu ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sanarwar ta bayyana marigayya Hajiya Asiya a matsayin mace mai ƙima wadɗa ta ƙarar da rayuwarta wajen taimakom ƴan uwanta, al'umma da kuma addini.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a yi mata Sallar jana'iza a yau, da misalin ƙarfe 2:00 na rana a gidan Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ke kan titin Miyangu jihar Kano.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, kakakin Ganduje ya ce:

"Cikin jimami muna sanar da rasuwar Hajiya Asiya Muhammad Gauyama, mahaifiyar Farfesa Hafsatu Abdullahi Umar Ganduje, matar shugaban APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje CON."
"Muna addu'ar Allah SWT ya jikan Hajiya Asiya Muhammad Gauyama ya sa ta huta, ya kuma baiwa iyalai da masoyanta hakurin jure rashinta.

Wannan na zuwa ne sa'o'i 24 bayan mataimamin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya yi rashin surukarsa.

Maryam Abubakar-Albishir, surukar Shettima ya rasu ne a Kano ranar Lahadi, 24 ga watan Yuni bayan fama.da jinya ta tsawon lokaci.

Za a yi jana'izar Maryam Abubakar, mahaifiyar matar mataimakin shugaban kasa, Nana Shettima, ranar Litinin a Kano kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Asali: Legit.ng

People are also reading