'Yan Bindiga Sun Saki Wata Alkalin Kotu Amma Sun Rike ’Ya’yanta 4, Suna Neman N150m
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Mai shari'a Janet Gimba, alƙali a kotun gargajiya dake Kaduna, wacce aka yi garkuwa da ita tare da 'ya'yanta a watan Yuni, ta samu 'yanci.
An ce har yanzu 'ya'yanta suna hannun waɗanda suka yi garkuwa da su bayan da aka gano cewa sun kashe ɗaya daga ciki mai shekaru 14, mai suna Victor.
Wannan lamarin ya matuƙar girgiza jama'a sakamakon rashin tausayin da 'yan bindigan suka nuna ƙarara, kamar yadda rahoton Daily Trustya bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dr. Musa Gimba, mijin alƙalin ya tabbatar da sakin matarsa amma ya bayyana cewa har yanzu waɗanda suka yi garkuwa dasu na buƙatar Naira miliyan 150 kafin su sako yaran.
Ya ce masu garkuwar sun bayar da wa'adi, inda suke buƙatar kuɗin fansar cikin kwanaki shida daga ranar Laraba kuma sun yi barazanar cutar da sauran yaran.
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da sakin alƙalin da kuma kisan Victor ga manema labarai.
Kakakin rundunar a Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatarwa da jama'a cewa hukumomi suna aiki ba dare ba rana domin ceto sauran waɗanda aka yi garkuwa dasu.
Ya ce jami'ai sun samu gawar Victor a Ungwan Bayero, kauyen Dutse, kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata, 2 ga Yulin 2024.
A wani labari na daban, mazauna jihar Kaduna sun fara gundura da lamarin 'yan bindiga inda wasu zaƙaƙurai suka fatattake wasu miyagun a lokacin da suka kai hari.
Wannan lamarin ya faru ne a ƙauyen rugar Sojidi da ke ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, kuma an ce mazauna garin sun jaddada kudurin cigaba da kare kansu.
Asali: Legit.ng