Home Back

Kyiv za ta tsaurara tsaro saboda barazanar Rasha

dw.com 2024/5/4
Rasha na zafafa kai hare-hare kan Ukraine
Rasha na zafafa kai hare-hare kan Ukraine

Hukumomi a Ukraine na cewa, za a tsaurara matakai a babban birnin kasar Kyiv sakamakon zafafa kai hare-haren makamai masu linzami da Rasha ke yi a baya-bayan nan. Rasha ta kai jerin hare-hare ta sama kan cibiyoyin makamashin Ukraine a makon da ya gabata a wani mataki na ramuwar gayya kan hare-haren da Kyiv ta kaddamar a yankunanta.

Karin bayani: Rasha ta kai sabbin hare hare wajen Kyiv

Guda daga cikin shugabannin tsaro na Kyiv, Serhiy Popko ya ce kwamittin tsaro na duba yadda ake gudanar da taruka da ma inganta tsaro a wajen taruwar jama'a. Ya kara da cewa, za a dauki wannan matakin ne sakamakon yadda makaman da dakarun Rasha ke harbawa ke yin barna cikin kiftawar ido. Sai dai kuma Popko ya bukaci mazauna Kyiv da su kwantar da hankulansu yayin da gwamnati ke iyakar kokarinta na tsare rayukan jama'a.

Ukraine dai na yawan mika bukatar samun karin tallafin makamai daga kawayenta na yammacin Turai domin ta kare kanta daga hare-haren makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka daga Rasha.

People are also reading