Home Back

Ba a Gama da Rigimar Sarautar Kano Ba, Gwamna Ya Yi Dokar Dakile Tasirin Sarakuna

legit.ng 2024/7/1
  • Ba a gama da rigimar sarautar jihar Kano ba, Gwamnan jihar Ogun ya kawo doka da zata rage matsayin sarakuna a jihar
  • Dapo Abiodun ya tabbatar da dokar da za ta dakile sarakunan gargajiya wajen shiga wata yarjejeniya da ya shafi filaye
  • Gwamna ya kuma kirkiri wasu ma'aikatu masu muhimmanci guda biyu a jihar domin bunkasa tattalin arziki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - Gwamna Dapo Abiodun ya kirkiro sabbin dokoki kan sarakunan gargajiya a jiharsa.

Abiodun ya yi dokoki da suka haɗa da dakile sarakunan gargajiya daga sanya hannu a yarjejeniya da ta shafi filaye.

Gwamnan ya kuma kirkiri sabbin ma'aikatu guda biyu a jihar, kamar yadda gwamanti jihar ta wallafa a shafinta na X.

Daga cikin ma'aikatun akwai ta kula da albarkatun cikin kasa a jihar da kuma ta tsare-tsare da yawon bude ido.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan a bangaren yada labarai, Kayode Akinmade ya tabbatar a yau Asabar 22 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dukkan masarautun gargajiya da ke fadin jihar an dakatar da su shiga wata yarjejeniya kan filaye da wani mutum ko kamfani."
"An dakatar da su daga ba da kofa ga kamfanoni ko hakar ma'adinai a fadin jihar baki daya."

- Kayode Akinmade

Gwamna Ahmed ya kirkiri doka kan sarakuna

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya samu sahalewa kan wata sabuwar doka game da hakimai.

Dokar za ta hana Majalisar sarkin Musulmi nada hakimai kai tsaye ba tare da sanin gwamnan ba kamar yadda ta saba.

Kafin wannan lokaci, Majalisar Sarkin Musulmi ne ke da ikon naɗa hakimi a fadin jihar baki daya ba da izinin gwamna ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading