Home Back

Harkar soji: Rasha na buƙatar makamai, Koriya ta Arewa na buƙatar ilimin ƙera makamai

bbc.com 2024/7/3
Shugaban Rasha Vladimir Putin da na Koriya ta Arewa Kim Jong Un

Asalin hoton, Reuters

A baya-bayan nan Amurka ta bai wa Ukraine damar amfani da makaman da Amurkar ta ƙera a yaƙin da take yi da Rasha
Bayanan hoto, A baya-bayan nan Amurka ta bai wa Ukraine damar amfani da makaman da Amurkar ta ƙera a yaƙin da take yi da Rasha

Yayin da samamen da Rasha ta kai wa Ukraine ke ƙara jan ƙafa, kimanin shekara biyu da rabi, Koriya ta Arewa da Rasha na ƙara neman taimakon juna.

Dr Nam Sung-wook, malamai ne a jami'ar Koriya ta Kudu, ya ce ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za a tattauna shi ne "ƙarin yawan makaman da Koriya ta Arewa ta haɗa waɗanda za ta samar wa Rasha."

Ya yi amannar cewa tattaunawar za ta iya taɓo batutuwa na dogon zango.

Akwai yiwuwar ƙasashen biyu su ƙulla yarjejeniyar yin aiki tare a harkar soji, ciki har da batun haɗa makamai.

Ana sa ran Koriya ta Arewa za ta buƙaci iya abinci da man fetur ba kadai, a madadin makaman da za ta bai wa Rasha ba.

Dr Nam ya yi hasashen cewa Koriya ta Arewa za ta buƙaci tallafin Rasha a ɓangaren kimiyyar sararin samaniya, bayan da ta gaza samun nasara a wani yunƙuri da ta yi na harba tauraron ɗan'adam na aikin soji zuwa sararin samaniya a watan Mayu.

Kasancewar tana da ƙwarewa a harkar sararin samaniya, Rasha za ta taimaka wa Koriya ta Arewa sosai wajen ganin ta samu nasarar harba nata taurarin ɗan'adam ɗin.

Haka nan ana sa ran Koriya ta Arewa za ta nemi agajin Rasha wajen samar da jirage masu tafiya a ƙarƙashin ruwa masu amfani da makamashin nukiliya.

Dr Nam na ganin cewa ba za a bayyana duk wata tattaunawa da ta shafi makaman nukiliya ba.

Mr Putin ya sha magana kan makaman ƙasashen Yamma da ake turawa zuwa Ukraine, inda ya yi barazanar cewa Rasha za ta iya duba yiwuwar amfani da makamin nukiliya.

Sai dai, Dr Nam ya ce duk wata haɗin gwiwa ko bayar da bayanai kan makamin nukiliya ga ƙasar Koriya ta Arewa ko ƙasashen arewa maso gabashin nahiyar Asiya, zai iya janyo martani maras kyawu daga ƙasashe maƙwafta da kuma wasu ƙasashen duniya kamar Amurka.

Saboda haka zai yi wahala a ga wani abu makamancin haka a lokacin ziyarar.

Tattalin arziƙi: Rasha na buƙatar ma'aikata, Koriya ta Arewa na buƙatar kuɗaɗen ƙasashen waje

Asalin hoton, Getty Images

Cikin gidan cin abincin ƴan Koriya ta Arewa na Koryo
Bayanan hoto, ‘Koryo’, wani gidan cin abinci na Koriya ta Arewa wanda a baya ake samu a Rasha

Akwai yiwuwar cewa Rasha da Koriya ta Arewa za su tattauna kan haɗin gwiwa game da tattalin arziƙi.

Dr Kang Dong-wan, malamin kimiyyar siyasa a jami'ar Dong-A ya ce babban abin da Koriya ta Arewa ke nema a yanzu shi ne "kuɗin ƙasashen waje daga leburori". Wannan na ƙara yiwuwar Koriya ta Arewa ta tura ƙarin ma'aikata zuwa Rasha.

A ɗaya ɓangaren kuma Rasha na neman leburori waɗanda za su yi aikin sake gina wuraren da yaƙi ya lalata da kuma farfaɗo da tattalin arziƙinta.

Dr Kang ya ce akwai yiwuwar shugabannin biyu su tattauna batun tura ma'aikata daga Koriya ta Arewa zuwa Rasha, kasancewar Rasha na fuskantar matuƙar ƙarancin leburori saboda tura mutane zuwa fagen daga a yaƙin da ake yi da Ukraine.

Sai dai takunkumin Majalisar Dinkin Duniya ya haramta wa Koriya ta Arewa tura ma'aikata zuwa aiki a ƙasashen ƙetare, kuma ya buƙaci duk wasu leburori ƴan Koriya ta Arewa su koma gida kafin ranar 22 ga watan Disamban 2019.

Saboda haka nan idan Rasha, wadda ke da kujerar dindindin a Kwamitin Tsrao na Majalisar Dinkin Duniya ta ɗauki leburori ƴan Koriya ta Arewa, hakan zai janyo surutai daga ƙasashen duniya.

Yanzu dai za a sanya ido kan yadda ƙasashen biyu za su ƙulla yarjeniyoyi na tattalin arziƙi ta yadda ba zai janyo suka da matsi daga ƙasashen duniya ba.

Musayar al'adu: Shin ana samun bunƙasar ziyarar buɗe ido a Koriya ta Arewa?

Asalin hoton, Reuters

Masu yawon buɗe ido a kan wata gada da ke kan rafin Yalu, wanda shi ne ya raba China da Koriya ta Arewa
Bayanan hoto, Masu yawon buɗe ido a kan wata gada da ke kan rafin Yalu, wanda shi ne ya raba China da Koriya ta Arewa

Rasha ta dawo da tsarin kai ziyarar buɗe ido na ƙungiya-ƙungiya zuwa Koriya ta Arewa, bayan dakatar da ziyarar a watan Fabarairun 2020 sanadiyyar annobar korona.

Haka nan a karon farko an dawo da sufurin jirgin ƙasa daga Koriya ta Arewa zuwa Rasha a ranar 6 ga watan Yuni bayan an dakatar na tsawon shekara huɗu.

Fiye da ƴan yawon buɗe ido na Rasha 400 ne suka ziyarci Koriya ta Arewa tsakanin watan Fabarairu zuwa Mayun 2024, kamar yadda gwamnatin yankin Primorsky Krai tya Rasha ta tabbar.

Wani kamfanin sufuri na Rasha, Vostok Intur, yana shirya ziyara ta kwana huɗu zuwa biyar zuwa Koriya ta Arewa kan kuɗi dalar Amurka 750 a shafinta na intanet.

Kamfanin ya bayyana cewa akwai tafiye-tafiye zuwa Koriya ta Arewa har zuwa cikin watan Satumba, ciki har da ziyarar tsaunin Paektu, da cibiyoyin adana tarihi na Koriya ta Arewa da kuma lokacin bukukuwan tunawa da yaƙin Koriya.

Kim Dong-yup ya ce "Yawon shaƙatawa ba hanya ce kaɗai ta samun kuɗaɗen shiga na ƙasashen waje ba amma tana kuma taka rawa wajen bunƙasa alaƙa tsakanin al'umma".

Ya ƙara da cewa ziyarar da mutanen Rasha ke kai wa Koriya ta Arewa zai taimaka wajen bunƙasa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu. Hulɗa tsakanin mutanen ƙasashen zai haɓɓaka dogaro da juna wanda hakan zai rage duk wani yuwuwar samun tankiya tsakaninsu.

Ya kuma ce ziyarar da ake kai wa a Koriya ta Arewa zai rage kallon da duniya ke wa ƙasar a matsayin wadda take a kulle kuma mai haɗari.

Sai dai akwai wasu lokuta a baya-bayan nan da aka soke wasu ziyarce-ziyarcen da aka tsara zuwa Koriya ta Arewa saboda tsoron takun saƙa da ke tsakanin ƙasar da Koriya ta Kudu.

A ƴan makwannin nan kamfanin tsara tafiye-tafiye na Rasha, Vostok Intur ya ruwaito cewa ya soke wata tafiyar yawon ziyara zuwa Koriya ta Arewa wadda aka tsara yi a ranar 31 ga watan Mayu, saboda rashin masu son zuwa.

Ƙarancin wuraren yawon buɗe ido da rashin dokokin hana ƴan ƙasar wajen tafiye-tafiye cikin ƴanci a ƙasar ta Koriya ta Arewa na daga cikin manyan ƙalubalen da ke hana ɓangaren yawon buɗe ido na ƙasar haɓaka.

People are also reading