Home Back

Gwamnatin Tarayya Za Ta Ci Bashin Dala Miliyan 500 Don Gina Hanyoyin Karkara

leadership.ng 2024/7/1
Tinubu Ya Nada Musa Aliyu A Matsayin Shugaban ICPC

Gwamnatin tarayya na neman rancen dala miliyan 500 daga Bankin Duniya, don bunkasa hanyoyi da kasuwancin noma a karkara a dukkanin fadin Nijeriya.

Hukumar bayar da lamuni ta kasa da kasa ta ce, ana sa ran wadannan kudade da za a bayar a matsayin rance, za su iya magance matsananciyar bukatar samar da kyakkyawar alaka a yankunan karkarar Nijeriya, inda a halin yanzu kimanin mutane miliyan 92 ke fama da wannan matsala ta hanyoyi.

Har ila yau, wannan bukata na kunshe ne cikin wani daftari na musamman da aka samar a hukumance, domin sake kyautata hanyoyi da samar da ayyukan yi ga yankunan karkara da kuma kasuwancin noma, wanda ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya ta samar.

Kazalika, shirin ya mayar da hankali ne wajen inganta hanyoyin shiga yankunan karkara, ta yadda za a inganta noma tare da wayar wa da mutane kai, domin su rungumi harkokin noma a matsayin sana’a don dogaro da kawunansu, wanda hakan ko shakka babu; zai taimaka wajen samar da ingantacciyar rayuwa ga al’ummar karkarar baki-daya.

Haka zalika, makasudin wannan aiki ya hada da inganta hanyoyi da samar da kyakkyawan yanayi a yankunan karkara, karfafa karfin hukumomi don gudanar da hanyoyin sadarwa na yankunan tare kuma da karfafa tushen hanyoyin samun kudi ga hukumomi, domin dorewar ci gaban yankunan karkarar da kuma jihohi.

Bugu da kari, wannan shiri na samar da hanyoyi da kasuwancin noma a karkara, zai dora ne a kan shirin nan da ake da shi na samar da hanyoyi da kasuwancin noma a karkara, wanda Bankin Duniya da Hukumar Raya Kasar Faransa ke tallafawa. Har ila yau, Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara ta Tarayya ce ke jagorantar aikin tare da sa ido a sashin kula da ayyukan gwamnatin tarayya.

Haka nan, daftarin ya yi nuni da cewa, “Hanyoyin Nijeriya na da matukar yawa, wanda yawan nasu ya kunshi kusan kimanin kilomita 194,000. Wadannan hanyoyi, sun hada da na gwamnatin tarayya; wadda take titina mai yawan kilomita 34,000, jiha ke da kimanin kilomita 30,000, sai kuma hanyoyin yankunan karkara da aka yi wa rigista kimanin kilomita 130,000.

“Duk da yawan wadannan titina da ake da su, hanyoyin shiga yankuna karkara a Nijeriya, idan aka yi la’akari da yawan al’ummar da ke zaune a cikinsa; za a tarar da cewa, hanyoyin su ne mafi lalacewa da kuma samun koma baya; wanda hakan ya yi sanadiyyar akalla mutane miliyan 92 mazauna karkarar, suka rasa kyawawan hanyoyi kwata-kwata; ta inda ko da noma suka yi, ba sa iya samun damar fitar da amfanin gonar tasu zuwa sauran kasuwanni.

“Kiri-kiri, an hana mutane shiga wadannan yankuna na karkara; musamman yankunan da masu fama da matsalar tattalin arziki suka fi yawa. Don haka, babu shakka wadannan abubuwa na nuna matukar muhimmancin fadadawa tare da inganta hanyoyin wadannan yankuna na karkara da kula da hanyoyin da kuma kadarorin sufurin da ake da su.”

An kiyasta jimillar kudaden wannan aiki a kan dala miliyan 600, wanda ake sa ran Bankin Duniya zai samar da kashi 83.33 cikin 100 na yawan kudaden da ake bukata.

Har ila yau, alkawarin kudaden sun haura kashi 79 cikin 100; sama da adadin da Bankin Duniya ya bayar da farko na dala miliyan 280, don aiwatar da ayyukan da suka shafi iyaye.

Shirin zai dauki nauyin manyan ayyuka guda uku, wadanda suka hada da farfado da hanyoyin karkara (dala miliyan 387), samar da kayayyakin bunkasa sauyin yanayi (dala miliyan 158), sai kuma aikin karfafa cibiyoyin gudanar da ayyuka (dala miliyan 55).

Kamar yadda aka gabatar da tsarin aikin, jihohin da ke son shiga tsarin aikin; wajibi ne su samar da cikakken asusun kula da hanyoyin motoci tare da kafa hukumomi da ma’aikata da kuma tanadar kudaden gudanarwa a cikin kasafin kudin jihar.

Kazalika, tsarin ya tabbatar da cewa, “Cancantar shigar jihohi karkashin wannan tsari, na bukatar tsarawa da kuma sanya kudirin asusun kula da titina a majalisar dokokin jihar. Sannan kuma, sabon aikin zai bukaci jihohi su samar da cikakken asusun kula da titina tare da hukumar kula da titinan da shugabannin gudanarwa da kuma ma’aikata, sai kuma kudaden gudanarwa wanda aka ware a cikin kasafin kudin jihar. Bugu da kari, shirin zai bayar da dama don habaka wakilcin mata a bangaren fannin sufuri.

Don haka, “Za a kasafta kudaden shirin ne bisa gasa tsakanin jihohin da ke samar da kulawa, musamman a bangaren da ya shafi zamantakewar al’umma, domin sake habaka hanyoyi da kuma kara inganta wadatar abinci a yankunan na karkara. Kazalika, za kuma a yi la’akari da jihar da ke nuna jajircewa wajen samar da ingantattun ayyuka gami da yiwuwar samar da kudade daga albarkatun da take da su”.

Haka nan, shirin ya tanadi aiwatar da tsare-tsaren sake inganta rayuwar al’ummar yankunan na karkara, ta hanyar bijiro musu da wadannan sabbin ayyuka; wadanda za su inganta rayuwarsu kai tsaye.

Ana kuma sa ran sama musu wadannan abubuwan alhairi masu matukar muhimmanci da suka rasa tare da tabbatar da ganin an kuma dauki matakan da suka dace, wajen tabbatar da biyan su diyyar filayen da aka karba a hannunsu kafin fara aiwatar da wannan aiki.

People are also reading