Home Back

Jarumar Kannywood, Hadiza Gabon Ta Ba ’Yan Mata Masu Shirin Shiga Fim Shawara

legit.ng 2024/6/25
  • Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon ta ba yan mata masu shirin shiga harkar fim shawarar hakuri a kan shi ya fi alheri
  • Hadiza Gabon ta fadi haka ne tare da bayyana cewa akwai tarin illoli ga 'yan mata idan suka shiga masana'antar Kannywood
  • Jarumar ta bayyana irin shawarin da take ba 'yan mata idan suka nemi ta musu hanyar shiga Kannywood domin fara sana'ar fim

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu da aka fi sani da Hadiza Gabon ta yi magana kan 'yan mata masu shirin shiga fim.

Hadiza Gabon ta ce akwai abubuwan da ya kamata yan mata su maida hankali a kai domin gina rayuwa mai kyau maimakon shiga fim.

Hadiza Gabon
Hadiza Gabon ta ba mata shawara kan shiga fim. Hoto: @adizatou Asali: Instagram

Jarumar ta fadi haka ne a wata hira da ta yi cikin tambaya da amsa kamar yadda shafin Bakori Celebrities ya wallafa hirar a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda suke ciki fim a halin yanzu

A cikin hirar da Hadiza Gabon ta yi, ta ce tana yiwa 'yan matan da suka riga suka fara harkar fim fatan gamawa lafiya.

Ta ce tun da sun riga sun fara ba abin da za ta musu sai fatan alheri amma tana gargadi ga masu shirin shigowa da su hakura.

Me za suyi maimakon shiga fim?

Hadiza Gabon ta ce yawanci idan yan mata suka mata tambayar neman shiga fim tana ba su shawarin yin aure ko karatu.

Ta ce yin aure ko komawa karatu shi ne abin da ya fi dacewa yan mata su yi domin gina rayuwa mai kyau a gaba.

Wane amfani ake samu a fim?

Har ila yau, jarumar ta bayyana cewa akwai amfani da ake samu a harkar fim domin ita ma ta samu daidai gwargwado.

Amma duk da haka ta ce rashin amfanin harkar yafi yawa a kan amfanin. Saboda haka ta ce yana da kyau duk wacce ta yi shirin shiga harkar ta zurfafa tunani.

Anyi ce-ce-ku-ce kan Hadiza Gabon

A wani rahoton, kun ji cewa shahararriyar jarumar Kannywood Hadiza Gabon ta saki sabon hotonta a dandalinta na soshiyal midiya kuma ya haddasa cece-kuce.

Legit ta gano cewa yayin da wasu ke yaba kyan jarumar, wasu na ganin sam rama bata yi mata kyau ba cewa ta fi a yar duma-daumar ta.

Asali: Legit.ng

People are also reading