Home Back

Yadda Gwamna Fubara ya gwangwaje maniyyatan jihar Ribas da kyautar $300 ƙarin kuɗin guziri

premiumtimesng.com 2024/7/1
Yadda Gwamna Fubara ya gwangwaje maniyyatan jihar Ribas da kyautar $300 ƙarin kuɗin guziri

Gwamnan jihar Ribas Simi Fubara ya ya raba wa Alhazan jihar $300 su yi ƙarun kuɗin guziri.

Da yake mika musu kuɗin a daidai kuma yana yi musu sallama kafin tashin su zuwa ƙasa mai tsarki, Fubara ya ce ya yi musu wannan ƙari ne domin Alhazan su iya kula da kansu a lokacin da suke aikin Hajji.

Ya hore su da su zama mutane nagari a kasar Saudiya sannan su yi wa jihar da Ƙasa baki ɗaya addu’a.

Shugaban hukumar Alhazai na jihar, ya godewa gwamnan bisa wannan karamci da ya yi musu sannan ya yi alkawarin maniyyatan za su zama mutane abin koyi a ƙasa mai tsarki.

Mutum 45 ne za su yi aikin Hajji na bana daga jihar Ribas yayin da dukkansu Alhazan banda mutum 5 gwamnati ce ta biya musu.

Hukumar NAHCON na dab da kammala jigilar maniyyata na bana inda zuwa yanzu ta kai sama da mutum 40,000 kasa mai tsarki.

People are also reading