Sabon Mafi Ƙarancin Albashi: Gwamnoni 17 Sun Aika Muhimmiyar Buƙata Ga Tinubu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Ogun - Kungiyar gwamnoni 17 na Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu sun nemi a bar kowace jiha ta biya albashi gwargwadon karfin tattalin arzikinta.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar bayan taro da kungiyar gwamnonin ta fitar jim kaɗan bayan ganawarsu a Abeokuta, jihar Ogun.
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito z gwamnonin sun nemi gwamnatin Bola Tinubu da a bar gwamnoni su tattauna da kungiyoyin kwadago na jihohinsu domin cimma matsaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar wadda take dauke da sa hannun dukkanin gwamnonin 17 ta ce hakan ne zai sa a samu daidaito tsakanin ma'aikata da gwamnatin jihohi.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnonin shiyyar Kudu sun bayyana shirinsu na samar da akalla 90,000 MW na wutar lantarki domin amfanin sama da mutane miliyan 90 na shiyyar.
Kungiyar ta yi amfani da dabarar samar da 1,000 MW na lantarki domin amfanin mutane miliyan daya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, inji rahoton Vanguard.
Kungiyar ta ce za ta yi amfani da sabuwar dokar da ta ba jihohi damar samar da nasu wutar lantarkin wajen ganin an inganta samar da wutar a shiyyar Kudancin kasar.
A wani labarin, mun ruwaito wani jigon jam'iyyar PDP, Rilwan Olanrewaju ya ce gwamnoni na da karfin ikon biyan sama da N100,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
A wata tattaunawa da Legit.ng, Mista Rilwan Olanrewaju ya ce duk da hakan, akwai bukatar a bar jihohi su biya abin da za su iya gwargwadon kudin da suka iya samu a kowanne wata.
Asali: Legit.ng