Home Back

An Bude Taron Majalisar Wakilan Jama’Ar Kasar Sin A Beijing

leadership.ng 2024/4/28
An Bude Taron Majalisar Wakilan Jama’Ar Kasar Sin A Beijing

Yau Talata da karfe 9 na safe, aka bude taron majalisar wakilan jama’ar Sin a babban dakin taron jama’ar Sin dake nan birnin Beijing. Wakilai kimani 3000 daga wurare da kabilu da sana’o’i daban-daban ne suke halartar taron, don sauke nauyin dake wuyansu na tsarin mulki da shari’a da dokoki.

A gun taron, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnati a babban zauren taruwar jama’a, inda ya ce gabanin manyan kalubalolin da ake fuskanta a kasashen duniya, da muhimman ayyukan yin kwaskwarima, da neman ci gaba, da tabbatar da zaman karko a cikin gida, JKS a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, ta hada kai da al’ummomin kabilu daban daban na kasar Sin, wajen warware matsalolin da suka gamu da su, yayin da suke sauke nauyinsu yadda ya kamata, kana sun cimma babbar nasara, da cimma burinsu a fannin raya tattalin arziki da zaman takewar al’umma.

A sa’i daya kuma, an cimma nasarar neman ci gaba mai inganci, da tabbatar da yanayin zaman karko na zamantakewar al’umma, lamarin da ya sa aka sami gagarumin ci gaba a fannin gina zamantakewar al’umma ta zamani bisa tsarin gurguzu a dukkanin fannoni.

Ya kuma kara da cewa, tattalin arzikin kasar ya bunkasa cikin yanayi mai kyau, inda ma’aunin tattalin arzikin GDPn ya zarce Yuan triliyan 126, adadin da ya karu da kaso 5.2 bisa dari. Kana, an samu ci gaba a fannin gina tsarin masana’antu na zamani, kuma masana’antun gargajiya sun samu kyautatuwa, yayin da sabbin sana’o’i suka bunkasa cikin sauri, kana, wasu manyan sakamakon da aka samu a fannin kirkire-kirkire sun kasance a sahun gaba tsakanin kasashen duniya.

Li Qiang ya kara da cewa, an samu sabbin sakamako a fannonin sabunta kimiyya da fasaha, kana, karfin yin kirkire-kirkire yana karuwa ba tare da tsayawa ba. A sa’i daya kuma, an zurfafa ayyukan yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje yadda ya kamata, yayin da ake inganta tushen neman bunkasuwa cikin tsaro. Haka zalika kuma, ana kyautata muhallin hallitu cikin yanayin zaman karko, yayin da ake kiyaye zaman al’umma yadda ya kamata.

Bugu da kari, ya ce, ba abu ne mai sauki ba, samun bunkasuwar tattalin arziki cikin shekarar da ta gabata, bisa kokarin da dukkanin al’ummomin kasar suka yi a fadin kasar, ba kawai an cimma buri a fannin raya tattalin arziki ba kadai, har ma an samu gaggarumin ci gaba a harkoki da dama. Sakamakon da aka samu, ya nuna cewa, a karkashin jagorancin kwamitin tsakiyar JKS da shugaba Xi Jinping, jama’ar kasar Sin ta nuna karfi da basira waje warware kalubalolin dake gabanta. Tabbas ne, kasar Sin za ta sami ci gaba na dindindin, yayin da ake kara samun makoma mai haske.

Majalisar wakilan jama’ar Sin mai wa’adin shekaru 5, hukumar koli ce a bangaren mulkin kasar. Ana gudanar da taron majalisar ne a ko wace shekara, inda ake tattaunawa da kuma yanke shawara kan manyan manufofi da dokoki da nada jami’ai.

Haka kuma, matakin koli ne da jama’ar Sin suke shiga harkokin kasa, lamarin dake bayyana manufar gudanar da siyasa ta dimokuradiyya a cikin tsarin mulki na gurguza mai sigar musamman na kasar Sin. Wannan taron dake gudana, ya kasance taro na biyu na majalisar wakilan jama’ar Sin karo na 14, wanda zai tattauna tare da nazari kan sabon rahoton ayyukan gwamnati, hakan ya sa yake jan hankalin bangarorin daban-daban.

Yayin taron na wannan karo mai wa’adin mako daya, wakilan jama’ar Sin za su saurari rahotannin gwamnatin tare da tattaunawa da gudanar da bincike, da kuma takaita ci gaban da aka samu a bara, da tsai da tafarkin raya kasa a sabuwar shekara.

A sa’i daya kuma, taron zai yi bincike kan rahoton bunkasuwar tattalin arziki da al’ummar kasar, da rahoton kasafin kudi na kwamitin tsakiya da na wuraren daban-daban, har ma da rahoton aiki na kotun koli da na hukumar koli ta bin bahasi ta jama’ar kasar.(Amina Xu\ Maryam Yang)

 
People are also reading