Home Back

Kano: Farfesa Ya Fadi Hanyar da Gwamna Abba Zai Yi Nasara, Ya Magantu Kan Fadar Nassarawa

legit.ng 2024/7/6
  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan masarautun Kano, Farfesa Farooq Kperogi ya yi tsokaci kan lamarin
  • Kperogi ya zargi Shugaba Bola Tinubu da tsoma baki cikin rikicin wanda ya kara rikita lamarin da kawo barazana
  • Farfesan ya kuma shawarci Gwamna Abba Kabir da ya bar shari'a ta yi aikinta inda ya gargade shi kan rushe fadar Nassarawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Farfesa Farooq Kperogi ya magantu kan rikicin sarautar jihar Kano da ake ciki yanzu.

Kperogi ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta nuna girma wurin ba bangaren shari'a yin hukuncin da ya dace.

Farfesan ya bayyana haka ne a rubutunsa na mako-mako da ya wallafa a shafin X a yau Asabar 22 ga watan Yunin 2024.

Ya zargi Shugaba Bola Tinubu da tsoma baki a lamarin sarautar jihar inda ya ce hakan kwata-kwata bai dace ba.

"Gwamnatin Tarayya ba ta da ikon shiga lamarin sarauta a kowace jiha a ƙasa, Femi Falana ma ya ce manyan kotunan Tarayya ba su da ikon daukar mataki kan abin da ya shafi masarautu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya kamata gwamnatin jihar Kano ta girmi wannan lamari ta bar bangaren shari'a ta yi abin da ya ce."
"Rushe gidan Aminu Ado Bayero ba abu ne mai kyau ba, ba na tare da hakan amma kamar rusau ya bi jinin jikin gwamnan."

- Farooq Kperogi

Abba Hikima ya magantu kan masarautun Kano

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen lauya a Kano, Abba Hikima ya yi tsokaci kan rigimar sarautar jihar da ake ciki.

Hikima ya ce a mahangar shari'a a yanxu Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano duba da hukuncin kotu kan rigimar.

Wannan na zuwa ne bayan Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci da wasu fitattun lauyoyi ke ganin akwai sarkakiya a ciki.

Asali: Legit.ng

People are also reading