Home Back

NNAMDI KANU YA SADUDA: ‘Idan aka sake ni zan magance matsalar tsaro cikin minti 2 a Kudu maso Gabas’ – Kanu

premiumtimesng.com 2024/4/29
AI BARI BA SHEGIYA BA CE: Nnamdi Kanu ya roƙi magoya bayan sa kada su tada buyagi a kotu

Gogarman ƙungiyar IPOB masu hauragiyar neman kafa ‘Biafra’, Nnamdi Kanu, ya bugi ƙirjin cewa matsawar aka sake shi, to zai kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta harɗe jihohin Kudu maso Gabas, na ƙabilar Ibo.

Kanu dai ya na tsare a magarƙamar SSS tun cikin Yuni, 2021, bayan an kamo shi daga ƙasar Kenya.

Yanzu haka ya na fuskantar tuhumar ayyukan ta’addanci a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Kanu ya bayyana haka a ranar Talata, inda ya ce matsalar tsaro na ci gaba da muni a yankin Kudu maso Gabas ne saboda ci gaba da tsare shi a hannun SSS.

“Duk wani mai tayar da zaune tsaye a yankin Arewa maso Kudu, zan iya dakatar da shi. A sake ni a gani. A cikin minti 2 kacal zan magance matsalar tsaro, ba ma a Kudu maso Gabas kaɗai ba, har ma a kudancin ƙasa baki ɗaya,” inji shi.

Kanu ya bayyana wannan buƙata a lokacin da yake zantawa da manema labarai a harabar Babbar Kotun Tarayya, a Abuja, ranar Talata.

Tuni dai bidiyon da ya yi wannan kalamin ya ke ta yawo a soshiyal midiya daban-daban.

Ya ce ya na zargin wasu jami’an gwamnati na da hannu a matsalar tsaron da ta addabi yankunan biyu, inda a cewar sa su na samun maƙudan kuɗaɗe a yankunan.

“Ai sun san idan aka saki Nnamdi Kanu, to wannan shekagantar zan iya kawar da ita a cikin minti 2 kacal. Saboda babu wanda zai iya ja da umarni na da faɗin yankin.”

Ya ce “masu kai hare-hare a yankin da sunan IPOB, ‘yan iska ne kawai maɓarnata, su ne ke kashe mutane wai da sunan su cimma kafa Biafra. Duk mai kashe mutane don ya kafa Biafra to mai laifi ne.”

 
People are also reading