Home Back

Yajin Aiki: Ƴan Kwadago Sun Dira Ofishin SGF a Abuja, Za Su Sa Labule da Jiga-Jigai

legit.ng 2024/7/3

FCT Abuja - Tawagar wakilan ƙungiyoyin kwadago a Najeriya sun isa ofishin sakataren gwamnatin tarayya a birnin Abuja yau Litinin, 3 ga watan Yuni.

Wata majiya ta bayyana cewa shugabannin ƴan kwadagon sun isa ofishin ne domin sa labule da wasu manyan jami'an gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Majiyar ta shaidawa jaridar Punch cewa:

"Zamu gana da wakilan gwamnatin tarayya a ofishin SGF, yanzu haka wakilan ƴan kwadago sun samu wuri sun zauna suna jiran karisowar su."

Sai dai majiyar ba ta bayyana sunayen wakilan gwamnatin da suka gayyato shugabannin kwadagon zuwa wannan taro ba.

Ku saurare mu...

Asali: Legit.ng

People are also reading