Home Back

Onana ya yi kuskuren da Burnley ta farke kwallo a Premier

bbc.com 2024/5/10
Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Mai tsaron ragar Manchester United, Andre Onana ya yi sanadin da Zeki Amdouni ya farke kwallo a wasan da suka yi 1-1 da Burnley a Premier League.

Kungiyoyin biyu sun kara a Old Trafford a wasan mako na 35 a babbar gasar tamaula ta Ingila, wadda saura karawa uku a kare kakar nan.

United, wadda ta kai wasan karshe a FA Cup ranar Lahadi, bayan nasara a kan Coventry City, ta ci Burnley kwallo a minti na 79 ta hannun Antony.

Kamar yadda Onana ya yi kuskure a wasa da Wolves, ya je ya yi kokarin naushin tamaula, domin ta bar gidansa, amma sai ya samu dan wasan Burnley.

To sai dai alkalin wasa, John Brooks bai ga abinda ya faruwa ba, sai mai kula da VAR, Peter Bankes ya ankarar da shi daga baya aka bayar da bugun fenariti.

Amdouni wanda ya shiga karawar daga baya, shi ne ya buga fenaritin, inda Onana ya fadi gefe guda, kwallo ya shiga ta daya bangaren.

Da wannan sakamakon Burnley, wadda take ta 19 teburi tana da tazarar maki biyu tsakaninta da Nottinghan Forest, wadda take ta hudu.

People are also reading