Home Back

Barkewar Kwalara: Ya Kamata A Dakatar Da Yin Kunu Da Zobo – Karamin Ministan Muhalli

leadership.ng 2 days ago
Barkewar Kwalara: Ya Kamata A Dakatar Da Yin Kunu Da Zobo – Karamin Ministan Muhalli

Sakamakon barkewar cutar kwalara a wasu sassan Nijeriya, gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Nijeriya su guji hada kunu da zobo da kuma fura domin takaita barkewar cutar.

Karamin ministan muhalli, Iziak Salako shi ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Salako ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su dauki matakan kariya kamar irinsu tsaftace muhalli a ko da yaushe da zubar da sahara a wuraren da ya kamata.

“Ko tabbatar da tsaftace ruwan da suke sha. Ruwa na daya daga cikin musabbabin barkewar cutar, ya kamata a dunga tafasa ruwan da ake amfani da shi a cikin gidaje.

“Ya kamata mutane su daina hada kayayyakin sha kamar irinsu kunu, zobo, nono, koko da sauran abubuwan sha sai dai idan har an dauki matakan kariya ta yadda ba za a kamu da cutar ba.

“A dunga wanke hannu da sabulu a ko da yaushe a cikin ruwan da ake wucewa, musamman bayan an fito daga bayi, a dunga wanke yara idan suka shiga bayi kafin su ci abinci da kuma bayan sun ci abinci da kuma lokacin da suka yi wasa da dabobi,” in ji shi.

Haka kuma ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi su kara kulawa da tsaftar muhalli a wurarin sayar da abinci da abubuwan sha da ke fadin kasar nan.

Wadannan wurare sun hada da kasuwanni, gareji, makarangtu, wuraren sayar da abinci, cibiyoyin wasanni, wuraren ibada da kuma sauran wurare da jama’a suke haduwa su ji abinci.

Salako ya ce daukan matakan kariya zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar kwalara da kuma samun damar kulawa da cutar. Ya kuma bukaci kwamishinonin muhalli da shugabannin kananan hukumomi su tallafa wa jami’an kula da tsaftar muhalli wajen tsaftace muhallin al’umma.

Ya kuma bukaci samun goyon bayan hukumomin kiwon lafiya da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da matakan da gwamnatin tarayya ta dauka.

People are also reading