Gwamnatin Jigawa Ta Yi Albishir ga Dalibai Masu Sha’awar Zuwa Karatu Kasar Waje
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana kudirin dawo da kai ɗalibai yan asalin jihar karatu kasar waje.
Gwamnan Umar A. Namadi ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar zartarwar jihar.
Mai taimakawa gwamnan jihar kan harkokin sadarwa, Garba Muhammad ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa Umar Namadi ya dauki matakin magance matsalolin da suka tsayar da shirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta bayyana cewa za a tura daliban ne zuwa kasar Singapore domin neman ilimi.
Gwamna Namadi ya ce za a tura daliban ne domin ganin Jihar Jigawa ta dawo da martabar da ta samu a harkar ilimi a shekarun baya.
Har ila yau gwamnatin ta bayyana cewa daliban za su karanci ɓangaren fasahar sadarwa ne a kasar Singapore.
Gwamna Namadi ya kara da cewa tun a baya Jigawa ta saba tura ɗalibai zuwa kasar domin karatu a bangaren fasahar sadarwa.
Gwamnatin ta bayyana cewa shirin ya samu tsaiko ne biyo bayan bashi da ya shiga tsakanin jihar Jigawa da kasar Singapore.
Amma a halin yanzu, gwamna Namadi ta ware kudi $220,000 domin warware bashin tun daga shekarar 2002 zuwa 2024.
Saboda haka a yanzu shirin zai cigaba inda dalibai za su rika zuwa karatu domin samun digiri na farko zuwa na biyu.
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa an samu ɓarkewar rikicin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kakakin rundunar ƴan sandan ya ce an raunata mutum biyar a rikicin da ya auku a dajin Hayin Kogi na ƙaramar hukumar.
Asali: Legit.ng