Home Back

Gwamnatin Jigawa Ta Yi Albishir ga Dalibai Masu Sha’awar Zuwa Karatu Kasar Waje

legit.ng 2024/7/7
  • Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya bayyana shirin dawo da kai dalibai yan asalin jihar karatu kasar waje domin bunkasa ilimi
  • Rahotanni sun nuna cewa majalisar zartarwar jihar ta amince da dawowa da shirin bayan tsaiko da ya samu na shekarun da dama
  • Gwamnatin jihar ta kuma bayyana matakan da ta dauka domin magance matsalolin da suka saka shirin ya samu tsayawa a baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana kudirin dawo da kai ɗalibai yan asalin jihar karatu kasar waje.

Gwamnan Umar A. Namadi ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar zartarwar jihar.

Umar Namadi
Gwamnatin Jigawa za ta kai dalibai karatu kasar waje. Hoto: Garba Muhammad Asali: Facebook

Mai taimakawa gwamnan jihar kan harkokin sadarwa, Garba Muhammad ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa Umar Namadi ya dauki matakin magance matsalolin da suka tsayar da shirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace kasa za a tura daliban Jigawa?

Cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta bayyana cewa za a tura daliban ne zuwa kasar Singapore domin neman ilimi.

Gwamna Namadi ya ce za a tura daliban ne domin ganin Jihar Jigawa ta dawo da martabar da ta samu a harkar ilimi a shekarun baya.

Me dalibai za su koyo a Singapore?

Har ila yau gwamnatin ta bayyana cewa daliban za su karanci ɓangaren fasahar sadarwa ne a kasar Singapore.

Gwamna Namadi ya kara da cewa tun a baya Jigawa ta saba tura ɗalibai zuwa kasar domin karatu a bangaren fasahar sadarwa.

Me ya kawo tsaiko ga shirin?

Gwamnatin ta bayyana cewa shirin ya samu tsaiko ne biyo bayan bashi da ya shiga tsakanin jihar Jigawa da kasar Singapore.

Amma a halin yanzu, gwamna Namadi ta ware kudi $220,000 domin warware bashin tun daga shekarar 2002 zuwa 2024.

Saboda haka a yanzu shirin zai cigaba inda dalibai za su rika zuwa karatu domin samun digiri na farko zuwa na biyu.

An yi rikici a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa an samu ɓarkewar rikicin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kakakin rundunar ƴan sandan ya ce an raunata mutum biyar a rikicin da ya auku a dajin Hayin Kogi na ƙaramar hukumar.

Asali: Legit.ng

People are also reading