Home Back

Mutane uku sun rasu yayin ciro Waya a cikin Masai da ceto mutum ɗaya a Kano – Hukumar Kashe Gobara

dalafmkano.com 2024/5/20

Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane uku, ciki har da Uba ɗan sa, a unguwar Ƴar Gwanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobarar PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyanawa gidan rediyon Dala FM, faruwar lamarin a daren jiya Lahadi.

Tunda fari dai mutum na farko mai suna Mallam Ɗan Juma mai laƙabin Black, wayar sa ce ta faɗa a cikin Masai, ya shiga domin ya cirota, sai dai gaza fitowar sa ke da wuya sauran mutane ukun suka bishi domin ceto shi lamarin da suma suka gaza fitowa.

Sauran mutane ukun akwai ɗan mutumin mai suna Ibrahim Ɗan Juma mai shekaru 35, sai na ukun mai suna Aminu T Gaye, da na huɗu mai suna Abbas Alhassan, ɗan shekara 28, amma shi an ciroshi a raye.

PSF Saminu Yusuf, ya kuma ce bayan faruwar lamarin ne jami’an su, suka ceto mutum na ƙarshe a raye, amma ukun farko basa cikin hayyacin su baki daya.

Ya ƙara da cewa tuni jami’an nasu suka miƙa mutanen a hannun jami’in hukumar ƴan Sanda, kuma babban baturen ƴan sanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano mai suna SP Ibrahim Lado, inda suka kai su asibitin ƙwararru na ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano.

People are also reading