Home Back

Me zai faru a wasan Bayern Munich da Arsenal a Champions League?

bbc.com 2024/5/19
Champions League

Asalin hoton, Reuters

Arsenal ta je Bayern Munich, domin buga wasa na biyu zagayen quarter final a Champions League da za su kara a Allianze Arena ranar Laraba.

Kungiyoyin sun tashi 2-2 a makon jiya a Emirates, kuma wasa na 14 da za su yi a Champions League, Bayern ta yi nasara bakwai da canjaras uku.

Bayern Munich na fatan amfana da wasan da za ta karbi bakunci a gida, domin kai wa 'yan hudun karshe a karon farko cikin kaka hudu.

Arsenal ta ci karo da koma baya ranar Lahadi, wadda Aston Villa ta doke ta 2-0 a Premier League, karon farko da ta yi rashin nasara a 2024 da canjaras daya.

Gunners ta hada maki 31 daga 33 da suke kasa a Premier League, amma ta koma ta biyu da maki 71, bayan da Manchester City ta dare teburin da maki 73.

City ta yi nasarar doke Luton Town 5-1 ranar Asabar a Etihad a Premier League karawar mako na 33, saura wasa shida a gaban City da Arsenal da kuma Liverpool.

Karon farko da Arsenal ta kai daf da karshe a Champions League shi ne a 2008/09.

Bayern Munich ta kwan da sanin daf take ta kare kakar bana ba tare da daukar kofi ba, kenan Champions League ne kadai a gabanta.

Tuni Bayern Leverkusen ta lashe Bundesliga na bana kuma na farko a karon farko a tarihi, wadda ta dauka ba tare da an doke ta ba a wasa 29 a jere, saura fafatawa hudu a kare kakar bana.

Labarin da ya shafi 'yan wasan Bayern da na Arsenal:

Bayern Munich za ta buga wasan ba tare da Alphonso Davies ba, wanda aka dakatar, yayin da Serge Gnabry da Kingsley Coman da Sacha Boey da Bouna Sarr da kuma Tarek Buchmann ke jinya.

Kyaftin Manuel Neuer da kuma Leroy Sane, wadanda ba su buga wa Bayern Munich karawar da ta doke Koln 2-0 ba ranar Asabar a Bundesliga, yanzu suna daga cikin wadanda za su fuskanci Arsenal.

Kamar yadda Mikel Arteta ya sanar ana tantama kan koshin lafiyar Bukayo Saka da Martin Ødegaard, wadanda suka bugu a karawar da Aston Villa ta ci Arsenal a Emirates ranar Lahadi - amma ana ci gaba da auna koshin lafiyarsu.

Tarihin da Bayern Munich take da shi a kan Arsenal a Jamus:

Champions League

Asalin hoton, Reuters

Bayern Munich ta yi rashin nasara daya daga shida a gida a Champions League da Arsenal da cin hudu da canjaras daya daga ciki.

Gabaki daya Gunners ta yi rashin nasara uku da ta je ta fuskanci kungiyar Jamus a bayan nan har da 5-1 da aka doke ta a Allianze cikin nuwambar 2014 da kuma Fabrairun 2017 shima 5-1.

Shi ne karon farko da aka ci Arsenal kwallaye da yawa a waje a gasar ta zakarun Turai.

Ba a yi nasara ba a kan Bayern Munich a gida ba a wasa 14 a gasar zakarun Turai da cin karawa 11 da canjaras uku.

Wasa daya ne Bayern ba ta zura kwallo ba a raga a karawa 28 baya a Allianze Arena shi ne 0-0 da Copenhagen a karawar cikin rukuni a kakar nan.

People are also reading