Home Back

NAHCON, Alhazai sun ƙaryata labarin wai ba a ba Alhazai abincin kwarai a Makka

premiumtimesng.com 2024/7/1
NAHCON, Alhazai sun ƙaryata labarin wai ba a ba Alhazai abincin kwarai a Makka

Hukumar Alhazai ta Kasa ta karyata labarin da wasu jaridu suka buga wai ana ciyar da alhazan Najeriya abinci mara kyau a kasa mai tsarki.

Baya ga hukumar, wasu Alhazai da kansu sun ƙaryata wannan zargi inda suke cewa ana neman a kawo ruɗani ne tsakanin mutane musamman waɗanda suke gida game da ayyukan hukumar.

Wani ne ba tare da ya tantance ba ya buga a shafinsa ta Facebook cewa wai ana ciyar da ƴan Najeriya abincin da ba shi da nagarta a Hajji.

Daga nan kuma sai wasu jaridu ba tare da yin bincike ba suka buga labarin cewa wai ba a ciyar da alhazan da abincin da ya dace duk da sun biya kuɗi masu yawa.

Hukumar Alhazai ta kasa ta karyata wannan batu tana mai cewa tana yin abinda ya kamata domin jin daɗin Alhazai.

Fatima Usara, babbar jami’an watsa labarai na NAHCON a ranar Talata ta bayyana cewa abin takaici ne ace wai jarida za ta ɗauki abu a yanar gizo ta buga ba tare da ta tantance ba.

” Hukumar Alhazai na yin iya kokarinta wajen tabbatar da Alhazan Najeriya sun samu duk ababen da suka bukata domin gudanar da ayyukan su cikin natsuwa da jindaɗi.

Wasu Alhazai da suka tattauna da PREMIUM TIMES a Madina sun yaba kokarin hukumar Alhazai ta kasa musamman a fannin samar da abinci mai kyau da ta yi.

Alhazan sun ce NAHCON ta taka rawar gani matuka wajen tabbatar da irin abincin da ake ba Alhazai ya zamo mai nagarta.

” Tsakani da Allah duk wanda ya ce NAHCON ba ta yi daidai ba game da abincin alhazai bai kyauta ba kuma bai yi mata adalci ba. Abinci ne mai kyau ake kawo mana a kullum da ruwan sanyi da lemo.

” Daidai gwargwado dai tunda ba a gidan ka kake ba wallahi ya yi. Allah ya sa a dore haka har karshe. Amma a sukan cewa wai ba a bada abincin kwarai ba gaskiya bane.

Haka kuma PREMIUM TIMES ta yi zagayen tabbatar da sahihancin abin a wasu dakunan cin abincin alhazai da ke masaukinsu a Madina.

” Abinda muka ga ni ya wadatar. Abinci ne har da tsokan nama kowani Alhaji ya ke samu safe da maraice. Da ya wa daga cikin su za kuga yadda suke cin abinci cike da farinciki suna nishaɗi da annashuwa.

A karshe dai hukuma jindaɗin Alhazan ta hori ƴan jarida da suka tantancewa da tabbatar da sahihancin labarai kafin su buga gudun kawo ruɗani a tsakanin jama’a.

People are also reading