Home Back

Mata masu juna biyu da matsalolin kiwon lafiya

dw.com 2024/6/26
Mai juna biyu
Mai juna biyu

Sai dai wasu gwamnatoci sun dauki matakin saukakewa mata masu juna hanyoyin da za su samu magunguna cikin sauki ko kuma ma kyauta a wasu jihohin. Mata da juna biyu a Najeriya sun koka da yadda magunguna gami da sauran kayan kula da taimakawa jariransu  inda duk sun yi tsada, abin da ya saka suka nemi hukumomi su dauki matakan da suka dace don ceto rayuwarsu da jarirai da suke shirin haifa.

Dubban Mata da ke da juna biyu sun ce ba sa iya sayen da yawa daga cikin magungunan da likitoci suka rubuta musu wadanda wasu na taimakon su da jarirai da ke cikin su wanda ke rashin samun sayen suka iya shafar rayuwarsu. Wannan damuwa da mata masu juna biyu suke nunawatare da mazajensu gami da masana lafiya da masu fashin baki kan yadda ya kamata a magance matsalar tsadar magungunan. Domin samun sauki magungunan zai yi tasiri wajen ceton rayuwar matan gami da jarirai.

People are also reading