Home Back

Ƴan Ta’adda 69 Sun Miƙa Wuya Ga Rundunar Tsaro Ta Haɗin Gwuiwa A Nijar Da Kamaru

leadership.ng 2024/7/24
Ƴan Ta’adda 69 Sun Miƙa Wuya Ga Rundunar Tsaro Ta Haɗin Gwuiwa A Nijar Da Kamaru

Ƴan Boko Haram su sittin da tara sun miƙa wuya ga rundunar haɗin Gwuiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) a Kamaru da Jamhuriyar Nijar tsakanin 1 zuwa 6 ga Yuli, 2024. Kakakin MNJTF, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, ya bayyana cewa mayaƙa 56, ciki har da Maza 13 da Mata da Yara 43, suka miƙa wuya ga Sojojin Sector 1 a Kamaru a ranar 6 ga Yuli.

A wannan ranar, an ceto iyalan ‘yan ta’adda 12, ciki har da Mata 5 da Yara 7. An miƙa mayaƙan da suka miƙa wuyan da kuma iyalan da aka ceto zuwa Sector 1, Operation Haɗin Kai, a Gamboru da Banki don ci gaba da ɗaukar mataki.

Haka kuma, a ranar 1 ga Yuli, wani ɗan Boko Haram mai shekaru 24 mai suna Tijjani Muhammad ya miƙa kansa ga Sojojin Sector 4 a Jamhuriyar Nijar. Ya mika kansa tare da bindigar AK-47, da babban gidan harsashi guda hudu, da kuma alburusai mau girman 7.62mm masu yawa, yana mai cewa ya tsere ne daga sansanin Boko Haram saboda ayyukan Operation Lake Sanity 2 da ake gudanarwa.

Ƴan Ta'adda

Ƴan Ta'adda

Laftanar Kanal Abdullahi ya bayyana cewa ƙaruwar yawan waɗanda ke miƙa wuya ya raunana ƙarfin ayyukan ƴan Boko Haram da kuma sanyaya gwuiwarsu.

Abdullahi ya ƙarfafa wa sauran mayaƙan Boko Haram da su yi amfani da wannan damar don miƙa wuya da ajiye makamansu domin samun zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Tafkin Chadi.

People are also reading