‘Burgar banza’: Hadimin Ganduje Ya Takalo Abba Kan Yunkurin Fatattakar Sarki Aminu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Salihu Tanko Yakasai ya yi aiki a gidan gwamnatin Kano, ya na cikin masu tofa albarkacin bakinsu kan halin da ake ciki.
Ana ta kai ruwa rana a game da sarautar Kano tun bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa hannu a doka, ya ruguza masarautu.
Salihu Tanko Yakasai ya yi magana a shafin X bayan an ji Mai girma Abba Kabir Yusuf yana kokarin ruguza fadar da ke Nassarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan siyasar ya yi martani yana mai cewa barazanar banza kurum gwamnan na Kano yake yi, babu yadda ya iya da karamar fadar.
Hadimin na Abdullahi Umar Ganduje ya zargi gwamnatin Abba da saba umarnin kotu.
A baya an ji yadda alkali Abdullahi Muhammad Liman ya zargi gwamnatin NNPP da bijire masa wajen nada Muhammadu Sanusi II.
"A daren jiya, aka kara tsaro sosai a fadar Nassarawa domin ba Sarki Aminu kariya a sakamakon barazanar kurum da gwamnatin jihar Kano ta yi,"
"Inda ta yi gigin rusa fadar (Nassarawa), duk da umarnin kotu cewa kowa ya dakata da batun."
"Wannan ma wani misalin yiwa kotu karon tsaye ne wanda ya zama ruwan dare a gwamnatin nan."
- Salihu Tanko Yakasai
A karshe Yakasai ya ba Abba shawarar cewa a matsayin gwamna, kyau ya zagaye kan shi da wadanda suka san abin da ya dace.
Ku na da labarin ana zargin Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta na neman cire Aminu Ado Bayero daga fadar Nassarawa da kafi da yaji.
Bashir Ahmaad ya ba gwamnan Kano shawarar ya daina tunanin amfani da kudin jama'a wajen ruguza fadar da Sarki na 15 yake zaune.
Asali: Legit.ng