Home Back

Yajin Aikin Kungiyoyin Ƙwadago Ya Ɗauki Zafi, an Rufe Ofishin Ministan Abuja

legit.ng 2024/7/4
  • Kungiyoyin kwadago sun rufe babbar kofar ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja wadda aka fi sani da kofar Minista a Abuja
  • Ginin ma'aikatar dai yana dauke da ofishin ministan Abuja, Nyesom Wike, da na ministan noma, Sanata Abubakar Kyari
  • Shugabar kungiyar kwadago ta JUAC, Comrade Rifkatu Lortyer, ta sha alwashin ci gaba da rufe ginin har sai an biya bukatunsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Yajin aikin kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC na ci gaba da dauakr zafi a babban birnin tarayya Abuja.

Kungiyoyin kwadago sun rufe babbar kofar ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja wadda aka fi sani da kofar Minista, inda a ka hana ma’aikatan shiga.

Zanga-zangar 'yan kwadago a Abuja
'Yan kwadago sun rufe ginin ofishin ministan Abuja. Hoto: @NLCHeadquarters Asali: Getty Images

An rufe ginin ofishin ministan Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Nation ta ruwaito 'yan kwadago na hukumar kula da babban birnin tarayya (FCTA) da na hukumar FCDA da kuma kungiyar kwadago ta hadin guiwa (JUAC) ne suka rufe ginin.

An ga ma’aikatan ma'aikatar suna shawagi a kusa da kofar yayin da shugabannin kwadago suka tilasta bin umarnin “babu shiga, ba fita.”

Shugabar JUAC, Comrade Rifkatu Lortyer, ta sha alwashin ci gaba da daukar matakin har sai an biya wa 'yan kwadago bukatunsu.

Kungiyar kwadago ta gargadi ma'aikata

Ta shawarci ma’aikatan hukumomin FCTA da FCDA da su zauna a gidajen su domin bin umarnin NLC da TUC in ji rahoton jaridar Vanguard.

Ginin ma'aikatar dai yana dauke da ofishin ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da takwaransa na harkokin noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari.

An ruwaito cewa jami’an tsaro a yanzu haka suna kofar shiga hukumomin FCTA da FCDA domin tabbatar da tsaro.

Asali: Legit.ng

People are also reading