Home Back

Ina So Na Ga Ina Kyautata Wa Iyayena Har Ma Da Bare

leadership.ng 2024/6/26
Ina So Na Ga Ina Kyautata Wa Iyayena Har Ma Da Bare

Maryam Abdullahi matashiya ce da ta yi karatun Boko mai zurfi, amma duk da haka ba ta tsaya neman aikin gwamnati ba ta tsunduma harkar kasuwanci, wanda kuma take samu tagomashi a kasuwancin nata.

Ta tattauna da wakiliyarmu BIKISU TIJJANI KASSIM a kan yadda take gudanar da harkokinta wanda a karkashinsa ta ce tana so ta ga tana kyautata wa iyaye har ma da bare da ba su hada komai da ita ba. Bugu da kari ta nusar da mata cewa su sani fa darajar ‘ya mace ita ce kan gaba da komai, don haka mata su kare mutuncinsu. Ga dai yadda ta kasance a tsakaninsu:

Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki

Suna na Maryam Abdullahi Auyo, ni ‘yar asalin Auyo ce a Jihar jigawa. Na yi firamare a Jihar kano, na yi sakandire a Jihar jigawa na yi jami’a a Jihar Kano.

Shin Maryam matar aure ce?

A’a ba ni da aure

Malama Maryam ‘yar kasuwa ce ko kuma ma’aikaciya ce?

Ni ‘yar kasuwa ce

Wanne irin kasuwanci kike yi?

Ina kasuwancin Online na ‘General Merchandise sunan Kamfanina Auyo’s Enterprise. Ina nan a Facebook, Instagram da sunan Auyo’s Enterprise da kuma Whatsapp.

Shin me kasuwancin naki ya kunsa, ma’ana kamar me da me kike sarrafawa?

Ina sayar da kayan sakawa, kimar su; Atamfa, Laces, Shadda, Yards, Abaya, Jallabiya, Hijabai, Kayan Bacci, Gyale, Sarka, Takalma, Kayan Kicin, Zanin Gado, Labulaye da dukkan abubuwan bukata, kuma har kayan aure ina hadawa.

Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwancin?

Babban burin kowa rufin asiri, ina so na ga ina iya kyautatawa iyayena da ‘yan uwa na, har ma bare, Allah ya raba mu da haram Amin.

Maryam ba ki fada mana matakin karatunki ba?

Ina da BSc Education Chemistry

Wane irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?

aminci shi ne komai a kasuwancin online, idan na hadu da wanda ba ya yarda da mutane saboda yanayin zamani shi ne nake fuskantar kalubale.

Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika cimma?

Alhamdulillah, cikin ikon Allah kasuwancina ya karbu ina kuma ganin ci gaba ta hanyoyi da dama, hakan babbar nasara ce a wajena.

Maryam Abdullah Auyo
Maryam Abdullah Auyo

Wane abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?

Na ga an sayi kayana, kuma kaya sun je hannun mai saye ba tare da an samu matsala ba sai ma yabawa da ya yi.

Dame kike so mutane su rika tunawa da ke?

Da alkhairi nake so a dinga tunawa da ni.

Ga karatu, ga kuma hidimomin sana’a, shin ta yaya kike samun damar gudanar da hutunki?

Ina hutawa a duk lokacin da na samu, lokacin da ban samu ba kuma, ba komai haka zan shiga harkokina, lafiya itace gaba.

Wacce irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?

Idan aka nemar min Aljannah da Albarka a wajen Allah.

Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?

Suna bani goyon baya dari bisa dari, ga dukkan abubuwan da nake sawa gaba sai dai Allah ya saka musu da alkhairi Amin.

Kawaye fa?

Kawayena mutanan kirki ne suma dukkan goyan baya ina samu a wajensu gaskiya, sai dai na ce Allah ya saka musu da alkhairi.

Me kike fi so cikin kayan sawa da kayan kwalliya?

Atamfa karshen adon Bahaushiya, kayan kwalliya kuma agogo.

A karshe wanne irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?

Darajar ‘ya mace tana gaba da komai, ya kamata mu kiyaye kanmu daga tozarci da wulakanci, mu kare mutuncinmu. Mu kuma ci gaba da addu’o’i.

Ban hakuri:

Muna bai wa masu karatu hakuri saboda kuskuren da aka samu a wannan shafi a makon da ya gabata, na hada hoton Maryam da wata tattaunawar da ba tata ba.

Don haka muka gyara muka sake wallafa tattaunawar.

Mun gode!

Edita

People are also reading