Rundunar Sojin Najeriya Ta Zabi Tudun Biri Domin Kai Tallafi Na Musamman
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna- Rundunar sojin Najeriya ta ayyana Tudun Biri a cikin wuraren da za ta kai tallafin lafiya domin bikin cika shekaru 161 da kafuwa.
Garin Tudun Biri dai nan ne jirgin rundunar sojin Najeriya ya sake bom bisa kuskure a watan Disambar bara.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Manjo Janar Matirenso Saraso ya bayyana dalilin zaben Tudun Biri wajen kai tallafin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamandan runduna ta daya da ke Kaduna, Manjo Janar Matirenso Saraso ya ce an zabi Tudun Biri ne da tallafin domin gyara alaka da ke tsakanin sojoji da mutanen garin.
Manjo Janar Matirenso Saraso ya kara da cewa hakan zai nuna cewa sojojin Najeriya suna gabatar da ayyukan jin kai ba wai yaki kawai suka iya ba.
Rundunar sojin Najeriya dai ta bayyana cewa tallafin zai shafi duba marasa lafiya a garin Tudun Biri da ba su magani.
Sojoji za su duba marasa lafiya daban daban domin ba su magani kyauta da kuma ba su wasu kayan da suke buƙata domin kula da lafiyarsu.
Manjo Janar Matirenso Saraso ya ce ya kamata mutanen Tudun Biri su fito kwansu da kwarkwata domin cin moriyar shirin.
Ya kuma yi kira garesu da su cigaba da ba sojojin Najeriya hadin kai domin tabbatar da tsaro a fadin Najeriya, rahoton PM News.
A wani rahoton, kun ji cewa watanni bayan kuskuren jefa bam kan ƴan Maulidi, Malam Uba Sani ya fara cika alƙawurran da ya ɗaukar wa kauyen Tudun Biri.
A watan Disamba ne sojoji suka jefa bam kan masulmi a taron Maulidi a kauyen, lamarin da ya yi ajalin mutane sama da 150.
Asali: Legit.ng