Home Back

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji

leadership.ng 2024/6/29
Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji

An farlanta wa Manzon Allah (SAW) yin Hajji a shekara ta shida bayan Hijira. Amma bai yi ba sai bayan Hijira da shekara 10.

Wasu malamai sun kawo hujjar cewa, bai yi Hajjin a shekara ta shida ba ne saboda a wannan shekarar Hajjin bai fado a cikin watan Zul-Hijja ba. Haka nan a shekara ta bakwai, da ta takwas, da ta tara har sai a shekara ta 10 wanda a cikinta ne lokacin yin Hajjin ya zo daidai da watansa.

A shekara ta tara, bayan ya nada Sayyidina Abubakar (RA) a matsayin Amirul Hajji a cikin watan Zhul-kida, sai ya sanar da duniya cewa badi zai je Hajji, duk mai son zuwa ya zo ya bi shi ya ga yadda zai yi (SAW).

Malamai sun kara da cewa dalilin jinkirtawan har ila yau yana da alaka da al’adar da Larabawa suka kasance suna yi ta jujjuya Hajjin a watanni. Misali, idan a wannan shekarar an yi Hajji a watan Ramadan, badi sai su ce a watan Shawwal za a yi. A kan hakan, sai Annabi (SAW) ya jinkirta har zuwa shekara ta 10; lokacin da Hajjin ya fada a watan Zhul-hajji. Shi ya sa a ranar Arfa ya ce ya gode wa Allah duniya ta kewaya ta dawo wurin da aka halicce ta, dama Hajji a Zhul-hajji ake yi.

Imam Muslim ya ruwaito Hadisi wanda salsalarsa ke saduwa da Sayyidina Ja’afarus Sadik (RA) zuwa Babansa, Sayyidina Muhammadu Bakir (RA) cewa, “Mun shiga wurin Jabir bin Abdullahi, sai yake tambayar mutanen da muka shigo ko su wane ne; har dai ya zo kaina. Na ce ma sa ni ne Muhammadu Bakir dan Hussaini. Sai ya yi wawake ya dora hannunsa a kaina ya kama gashin kaina, ya kwance maballin rigata na sama sannan ya kwance na kasa, sai ya dora hannunsa a kirjina (don ya tuna irin kirjin Ma’aiki (SAW)), ni saurayi ne a wannan lokacin.

Daga nan ya ce “lale da dan dan’uwana, tambayi abin da kake so. Na san kai malami ne, ilimi kake nema, so kake ka ji labarin kakanninka. Na zauna da Manzon Allah (SAW), na zauna da Sayyidina Aliyu, na zauna da Sayyidina Hassan da Hussaini, na zauna da Sayyidina Aliyu Zainul-Abidina (Babanka), don haka tambayi duk abin da kake so.” Shi (Jabir) makaho ne a lokacin, ina cikin tambayarsa kenan sai lokacin sallah ya yi, sai ya tashi a cikin wani dan mayafi da ya daura kuma ya yafa.

Amma saboda kankancinsa duk lokacin da ya jefa shi a kafada sai ya fado alhali kuma ga babban mayafinsa a rataye a kantarsa. Sai ya yi mana sallah. Bayan gamawa na tambaye shi ya ba ni labarin Hajjin da Annabi (SAW) ya yi na karshe. Sai (Jabir) ya yi ishara da hannunsa tare da maganarsa, ya kure yatsunsa guda tara ya ce, “Annabi (SAW) ya zauna shekara tara bai yi Hajji ba, sannan ya yi izini a shekara ta 10 cewa zai yi Hajji a shekarar, sai mutane masu yawa suka taho Madina a shekarar ta 10, kowa yana so ya ga yadda Annabi (SAW) zai yi Hajji don ya yi koyi.

Sai muka fita tare da shi (SAW) har muka zo Zul-hulaifa aka yi ta shirin harama. Sai matar Sayyidina Abubakar Asma’u bintu Umaisin ta haifi dan da ya sa ma sa sunan Annabi (Muhammadu bin Abubakar). Ta aika (jaririn) zuwa wurin Annabi (SAW) kuma ta tambaye shi cewa ga shi ta haihu, yanzu ya za ta yi (da batun Hajjinta)? Annabi (SAW) ya aiko mata da amsar cewa, “Ke ma ki yi wankan harama da Hajji, daga nan ki yi kunzugu (Nafkin, wannan yana nuna macen da ba ta tsarki idan za ta yi Aikin Hajji dole sai ta yi wankan harama duk da cewa ba za ta yi sallah ko ta shiga Ka’aba ba).

Sai Manzon Allah (SAW) ya yi sallah a Masallacin Zul-hulaifa, daga nan ya hau rakumarsa (Kaswa) har ta daidaita da shi a sarari. Sai na duba sarari; ga mahaya nan da masu tafiyar kasa a ko ina dama da hagunsa (SAW) iya ganina. Annabi (SAW) kuma yana tsakiyar yara (matasa), sai ya yi niyya ya daga muryarsa yana cewa “Labbaikal lahumma labbaik… zuwa karshe”, (ma’ana amsawarka ya Allah, ka ce in je Hajji kuma na amsa).

Mutane su ma suka amsa. Mu dai (in ji Sayyidina Jabir), Hajji kawai muka yi niyya a lokacin, a haka muka rinka tafiya tare da Annabi (SAW) har muka zo Makka muka shiga Masallaci. Farkon abin da Annabi ya fara yi bayan mun shigo Masallacin shi ne sumbantar Dutsen Hajarul As’wad. Sai ya fara Dawafi tare da sassarfa muma muna yi, har sai da aka yi zagaye uku sai (Annabi SAW) ya koma yin tafiya har aka yi zagaye hudu.

Bayan haka, Annabi ya zo daidai Mukamu Annabi Ibrahim (AS) sai ya tsaya a bayansa, ya sa Mukamun a gabansa (tsakaninsa da Ka’aba), ya karanta ayar da ke cewa, “… Sai ku riki Mukamu Ibrahim a matsayin wurin Sallah”.

Daga nan ya yi Sallar Nafila raka’a biyu, a ta farko ya karanta Kulya Ayyuhal Kafiruun, a ta biyu ya karanta Kulhuwallahu Ahad. Sai Annabi (SAW) ya koma ya sake sumbantar Hajarul As’wad. Daga nan ya fita zuwa kofar Safa, yayin da ya hau kan Safa sai ya karanta ayar da ke cewa, “Hakika Safa da Marwa alamomi ne daga alamomin Addinin Allah…” ya ce “Na fara da wanda Allah ya fara ambata”, da ya hango Ka’aba sai ya ce “La’ilaha illallahu wahdahu la shariykalahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli sha’in kadiyr. La’ilaha illallahu anjaza wa’adahu…”

Sannan ya yi addu’a (idan Alhaji ya haddace wannan ya karanta, idan bai haddace ba ya karanta Subhanallahi wal-Hamdulillah wal-Lahu akbar ko ya yi ta fadin la’ilaha illallah). Bayan Annabi (SAW) ya gama addu’ar sai ya sake maimaita wannan addu’ar sau uku, sai ya sauko daga Safa ya taho Marwa. A lokacin da ya zo kwari (tsakiyar Safa da Marwa), sai ya yi sassarfa (a nan maza ke yin sassarfa, ban da mata).

Da ya hau kan Marwa sai ya tsaya ya yi addu’a kamar yadda ya yi a Safa. Haka ya rika yi har ya kammala Sa’ayin a Marwa. Sai Annabi (SAW) ya ce “Idan na sa gaba kan abu ba na dawowa, da ban zo da abin hadaya ba, sai in yi Hajjin Tamattu’i in mayar da wannan Hajjin Umura. Amma yanzu duk wanda bai zo da abin hadaya ba, ya mayar da wannan Hajjin ya zama Umura (ya kwance haramarsa, ya yi aski)”. Sahabbai suka ce “Ya Rasulallahi bai fi kwana hudu a yi Arfa ba”, Annabi (SAW) ya ce “Ku cire haramar kawai, ku yi aski.”

“Sai Surakatu Ibn Malik Ibn Ju’ushamu ya mike ya ce “Ya Rasulallahi, wannan hukunci na yanzu (na mayar da Hajji Umura saboda rashin zuwa da abin hadaya), na wannan shekarar ne kawai ko na ko wace shekara ne?”, sai Annabi (SAW) ya shigar da yatsunsa wasu a cikin wasu ya dunkule su ya ce “Umura ta shiga cikin Hajji sau biyu, bari ma dai Umura ta shiga cikin Hajji har abada.”

Sai Sayyidina Aliyu (RA) ya zo daga Yeman da rakuma, yana zuwa ya shiga wurin iyalinsa, ya tarad da matarsa (Sayyida Fadima (AS)) ta yi ado, ya tambaye ta game da hakan alhali ta riga ta yi harama da Hajji? Sai ta ce ma sa: “Babana (SAW) ya ce in yi.” Sayyidina Aliyu ya fada mana a Iraki (in ji Jabir) cewa, “Sai na tafi wurin Babanta don na kai kararta bisa abin da ta aikata kuma in tambaye shi (SAW). Da na fada ma sa, sai Annabi (SAW) ya ce “ta yi gaskiya, ta gaskiya.

Kai me ka ce da za ka yi haramar Hajji?” sai na ce, “Cewa na yi; na yi niyyar harama da abin da Annabi ya yi harama da shi.”, daga nan Annabi (SAW) ya ce “Ni ina da abin hadaya, don haka ba zan warware harama ba”. Sayyidina Aliyu ya ce “to nima na zo da rakuma” sai Annabi (SAW) ya ce “to ka shiga cikin hadayata”, sai adadin rakuman da Annabi ya zo da su da wanda Sayyidina Aliyu ya zo da su suka kai yawan guda 100. Daga nan mutanen (da ba su zo da abin hadaya ba) duk suka warware Hajjinsu sai Annabi (SAW) kawai da wadanda suka zo da abin hadayarsu (Sayyidina Aliyu da wani Sahabi guda daya).

“Haka aka zauna har zuwa ranar takwas ga wata, sai Manzon Allah (SAW) ya hau rakumarsa zuwa Mina inda ya yi Sallolin Azahar, La’asar, Magriba, Isha’i, Asubahi duk a can. Da gari ya waye bayan rana ta fito, Annabi (SAW) ya yi umurnin cewa a je a kafa ma sa rumfarsa a Arfa. Annabi (SAW) ya tafi Arfa ya shiga cikin rumfarsa, bai fito ba har sai lokacin da rana ta gota, sai ya bukaci a dora wa rakumarsa sirdi, ya hau aka biyo bayansa zuwa kwarin nan (wurin da Masallacin Namira yake a yanzu) ya yiwa mutane huduba… Bayan ya kammala sai Bilal ya yi wazna aka fara Sallah. Annabi (SAW) ya hada Azuhur da La’asar (Kasaru), daga nan ya hau rakuminsa ya dawo Arfa. Ya kalli Alkibla ya yi ta Zikiransa yana tsaye har zuwa lokacin da rana ta fadi.

Sai ya sa Usamatu Ibn Zaidu ya hau bayansa a kan rakuminsa ya kama hanya yana tafiya ba tare da sauri ba yana mai nuni da hannunsa cewa mutane su tafi sannu a hankali, har aka zo Muzdalifa. Annabi (SAW) ya yi mana Magriba da Isha’i da kiran sallah daya, ikama guda biyu amma Isha’i kasru aka yi. Ana kammala sallar sai Annabi (SAW) ya kwanta ba tare da ya yi nafila ko daya ba har zuwa Asalatu. Sannan ya tashi ya yiwa al’umma Sallar Asubahi.

“Daga nan ya hau rakumarsa zuwa Mash’aril Haram (wani Masallaci kafin isa wurin Jifan Shaidan). Ya tsaya a nan yana Kabbarbari har zuwa lokacin da gari ya yi sarari, sannan ya mika hanya inda ya goyo Fadlu Dan Abbas a rakuminsa… Har suka iso Badnil Muhassar (wurin da aka hallaka giwaye) inda ya dan yi sauri har ya shige wurin ya bi ta hanyar da ake isa wurin Jifar Jamratul Akba ya yi Jifa da tsakuwa bakwai.

Sannan bayan ya yi addu’a sai ya tafi wurin hadayarsa ya soke rakumi 63 da hannunsa, sai ya mika wa Sayyidina Aliyu mashi ya soke ragowar. Kuma ya yi horo a yanko nama kadan a ko wane rakumi aka dafa ya ci. Daga nan ya yi aski, sai kuma ya hau abin hawansa zuwa Makka ya yi Dawafin saukowa daga Arfa (Dawaful Ifada). Sannan ya yi Safa da Marwa. Bayan ya kammala sai ya je Rijiyar Zamzam, ‘ya’yan Abdulmuddalibi suka bashi guga ya sha.” Wannan shi ne ruwayar Hajjin Annabi (SAW) da Sayyidina Jabiru (RA) ya ruwaito.

Malamai sun yi bayanin cewa a cikin wannan Hadisin akwai hukunce-hukuncen Aikin Hajji sama da guda 100 a ciki.

People are also reading