Home Back

Ko yarjejeniyar tsagaita wuta na kawo ƙarshen yaƙi?

bbc.com 2024/10/5
Israelis demanding a ceasefire in a demonstration

Asalin hoton, Getty Images

Ana cigaba da yunurin ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza tsakanin Isra'ila da Hamas.

An fahimci cewa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na ta tattauna tayin zaman lafiyar da ministocinsa.

Sai dai ko tsagaita wutar zai kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Gaza na dindindin, ko kuwa na ɗan lokaci ne kawai?

Me tsagaita wuta ke nufi?

A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), babu wata ma'ana ɗaya tilo da aka amince da ita a matsayin ma'anar tsagaita wuta - ko kuma ceasefire a Turance - duk da cewa an samo kalmar ce daga harshen soja da ke nufin umarnin dakatar da buɗe wuta, wadda kishiyar umarnin buɗe wuta ce.

Za ta iya nufin duk wani abu da ɓangarorin da ke yaƙi da juna suka amince a tsakaninsu yayin tattaunawa.

Kazalika, akan maye gurbin kalmar da wasu kamar "tsahirtawa" (truce) ko "dakatarwa" (armistice).

Saia dai MDD ta ce akwai bambanci tsakanin kalmomin "ceasefire" (tsagaita wuta) da kuma "cessation of hostilities" (dakatar da buɗe wuta).

Ta ce "cessation of hostilities" (dakatar da buɗe wuta) na nufin wata yarjejeniya ba a hukumance ba da za ta dakatar da yaƙi.

"Ceasefire" (tsagaita wuta) kuma an fi yin ta a hukumance kuma akan ƙulla ta bisa sharuɗɗan da za su fayyace za a aiwatar da ita.

Asalin hoton, Getty Images

Wata yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla a 1993 ta kai ga kawo ƙarshen yaƙi tsakanin gwamnatin Liberiya da 'yantawayen National Patriotic Front of Liberia (hotonsu a sama)
Bayanan hoto, Wata yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla a 1993 ta kai ga kawo ƙarshen yaƙi tsakanin gwamnatin Liberiya da 'yantawayen National Patriotic Front of Liberia (hotonsu a sama)

Misali, an kawo ƙarshen yaƙin basasa a Liberiya a 1993 lokacin da gwamnati ta ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙungiyar National Patriotic Front of Liberia da kuma United Liberation Movement of Liberia for Democracy.

Duka ɓangarorin sun amince su daina yin safarar makamai, su daina kai wa sojoji hari, su daina tunzira fitina, da kuma daina dasa abubuwan fashewa.

Shin tsagaita wuta ta dindindin ce ko kuma ɗan lokaci?

Za ta iya zama duka biyun, a cewar MDD.

Wani zubin ɓangarorin da ke yaƙi da juna za su iya ƙulla yarjejeniya ta ɗan lokaci, ko masomi, ko kuma dakatar da yaƙin gaba ɗaya.

Akan yi hakan ne domin daina tayar da fitina ko kuma ba da damar gudanar da ayyukan agaji.

Lokacin da Isra'ila da mayaƙan Falasɗinawa na Hamas suka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin 24 zuwa 30 ga watan Nuwamban 2023, Hamas ta saki mutanen da take garkuwa da su 105 a madadin fursunoni 240 da Isra'ila ta saki.

Za kuma a iya ƙulla yarjejeniya a matsayin share fage, wadda za ta ba da damar fara tattaunawar da za ta samar da hanyoyin da za a kawo ƙarshen yaƙi gaba ɗaya.

Asalin hoton, Getty Images

Yarjejeniya ta ɗan lokaci da aka ƙulla tsakanin Habasha da Eritrea a shekarar 2000 ta kai ga dakatar da yaƙi baki ɗaya
Bayanan hoto, Yarjejeniya ta ɗan lokaci da aka ƙulla tsakanin Habasha da Eritrea a shekarar 2000 ta kai ga dakatar da yaƙi baki ɗaya

A watan Yunin 2000, Habasha da Eritrea sun ƙulla yarjejeniya domin dakatar da yaƙi da zimmar kawo ƙarshensa daga baya.

Sai dai kuma, za a iya cigaba da yaƙi idan aka gaza cika alƙawurran da yarjejeniyar ta ƙunsa.

MDD ta yi yunƙurin ƙulla yarjejeniya a lokuta da yawa domin kawo ƙarshen yaƙin basasa a Lebanon - a 1978, da 1981, da 1982. Amma kuma yaƙin ya ci gaba bayan kowace yarjejeniya, inda har sai a 1990 ya tsaya tun daga 1970.

Asalin hoton, Getty Images

Wata yarjejeniya a 1998 ta buƙaci ƙungiyoyin IRAda magoya bayansu su zubar da makamai a ƙasar Ireland ta Arewa
Bayanan hoto, Wata yarjejeniya a 1998 ta buƙaci ƙungiyoyin IRAda magoya bayansu su zubar da makamai a ƙasar Ireland ta Arewa

Misali, yarjejeniyar da aka ƙulla a wata Juma'a ta buƙaci ƙungiyar Provisional IRA da ƙawayenta a ƙasar Ireland ta Arewa su zubar da makamansu.

Yarjejeniyar ta kuma ƙunshi wasu saɗarori da zimmar ƙarfafa haɗin kan da ake da shi a yankin, kamar barin iyakar Ireland ta Arewa da Jamhuriyar Ireland a buɗe kuma ba tare da karɓar wani haraji ba.

Waɗanne irin tsagaita wuta ake da su na ɗan lokaci?

Asalin hoton, Getty Images

Yayin tsagaita wuta "ta ɗan lokaci" a Gaza, an saki Isra'ilawa 105 a madadin fursunoni Falasɗinawa 240 da Isra'ilar ta saki
Bayanan hoto, Yayin tsagaita wuta "ta ɗan lokaci" a Gaza, an saki Isra'ilawa 105 a madadin fursunoni Falasɗinawa 240 da Isra'ilar ta saki

Isra'ila da Hamas sun kira tasu tsagaita wutar a watan Nuwamban 2023 da "ta ayyukan agaji".

Akan yi amfani da irin wannan yarjejeniyar don daƙile tashin hankali ko kuma taimaka wa mutanen da yaƙin ya shafa.

Misali, gwamnatin Sudan ta amince da tsagaita wuta da ƙungiyoyi biyu, Sudan Liberation Movement da kuma Justice and Equality Movement, wadda ta kawo ƙarshen yaƙin Darfur na kwana 45 don bai wa ƙungiyoyin agaji damar kai kayan tallafi ga mutane.

A 2004, bayan guguwar tsunami ta afka wa Indonesia, gwamnatin ƙasar da ƙungiyar Free Aceh Movement sun sanar da tsagaita wuta saboda a kai wa mutane agaji a inda ake yaƙin.

Akwai kuma yarjejeniyar da aka ƙulla don dakatar da faɗan a wani yanki, wadda aka kira tsagaita wutar yanki.

A 2018, MDD ta shiga tsakanin gwamnatin Yemen da mayaƙan ƙungiyar Houthi don daina yaƙi a tashar ruwan Hodeida da ke kusa Kogin Maliya domin kare rayukan mazauna yankin.

People are also reading