Home Back

Jami'an filin jirgin Heathrow na London za su yi yajin aiki

dw.com 2024/5/1
Hoto: Steve Parsons/empics/picture alliance

Daruruwan jami'an tsaron kula da iyaka na filin jirgin saman Heathrow da ke birnin London, za su fara yajin aiki a cikin wannan wata na Afirilu, sakamakon kokawa da suka yi kan halin da yanayin aikinsu ke ciki.

Ma'aikatan su sama da 300, za su fara yajin aikin ne a ranar 29 ga watan, zuwa 2 ga watan Mayu mai kamawa, in ji babbar sakatariyar kungiyar kwadagonsu Fran Heathcote.

A shekarar 2022 da jami'an suka tsunduma irin wannan yajin aiki, gwamnatin Burtaniya ta sanya sojoji gudanar da aikin binciken fasfo din matafiya, a filin jirgin saman na Heathrow, wanda ke zama daya daga cikin manyan filayen jiragen sama da suka fi fice a duniya.

People are also reading